Ahmad shanawa's New Born Baby

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitaccen mawaki jarumi kuma mataimaki na musanman ga gwanar jihar Fulato wato "Ahmad shanawa" (baban chakwai), ya samu karuwa ta ya mace a ranar Juma'a 13 ga watan feburerun nan da muke ciki da musalin karfe 11 da minti 10 na dare.

Mawaki ya wallafa a shafin sa na Instagram ne inda ya baiyana cewa Alalh ya azurta shi da samun ya mace kuma da yar da mahaifiyar duk su na cikin koshin lafiya. Darurruwan masoyan mawakin ne da abokan sana'nar sa ne su ke cigaba da taya shi murna da farin cikin tare da masa fatan alheri a shafukan su na sada zumunci.

Shanawa dai mawaki ne da mata ke kaunar salon wakokin sa musanman yan mata wanda wakar ta sa tafi karkata akan su. Wa su daga cikin wakokin da su ka fito da mawakin sun hadar da "Baby Chakwai", " Ai yi kamat" da dai sauran su, haka zalika ya yi wakoki da mawaka irin su "Tinkin mai gashi" da dai sauran su.

Mawakin dan asalin Jos, na daya daga cikin mawakan da masoyan su da dama ba su san su na da aure ba sai a bayan ya wallafa hoton haihuwar da ya samu a Instagram, sai dai akwai alamun mawakan su na boye rayuwar auran su ne a bisa dalilan da su kadai su ka barwa kan su masaniyan yin hakan.

Amma akwai yuwar fadada bincike dan sanin mai nene dalili, dan baiyana wa ma su bibiyan shafin mu abun da binciken mu ya gano.

Also Read

Yakubu Muhammad New Series Release

News on Namenj and Hamisu Breaker new song

An yi wa maganar jarumi Momo mumunar fahimta a radiyo

An yi bikin zagayowar ranar haihuwar mawaki Umar M. Sharsef

Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Na Fara Film Ina Dan Wata Hudu a Duniya: Amude Booth

Leave your comment