News on Namenj and Hamisu Breaker new song

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Babban mawakin Nigeria Mr Eazy ya sanar wa duniya fitowar sabuwar wakar da mawaki Namenj da ke karkashin sa ya yi tare da mawaki Hamisu breaker. Mawakin ya wallafa wannan sanarwan ne a shafin sa na Twitter tare da baiyana wa su aiyukan da mawakan sa su ke shirin fitarwa a cikin wannan sabuwar wakar Feburerun 2021 da mu ke ciki.

Namenj wanda ya shahara a fannin hawa kan wakokin wa su mawakan na da a cikin salon zamani, ya yi fice ne a wakar Umar M. Shareef da ya hau a shekarar 2019.

Wanda jarumai da dama su ka dinga daura fefen bidiyan a shafukan su na sada zumunci, kuma daga busani shi ma ya fara fitar da na sa wakokin da su ma su ka ja hankalin masoyan sa. Namenj dai mawaki ne a karkashin kwanfanin Empower Africa wanda mallakan shahararren mawaki Mr Eazy ne, a karkashin kwanfanin akwai fitaccen mawaka irin su Joeboy da kuma Dj Ab daga Arewacin Nigeria.

Wannan sabuwar wakar dai da ko sunan ta mawakan ba su baiyana ba, daga dukkan alamu za ta yi tashe matuka dan ganin yadda ta fara jan hankalin masoya, musanman ganin yadda mawakan biyu ke kara bungasa da cigaba a duniyar masoya nishadi.

Duk da kasancewar Namenj a karkashin kwanfanin Mr Eazy ya ke a halin yanzu, mawakan biyu ba su taba waka tare ba ko kuma fitowa ta musanman a fefen bidiyo daya. Za mu cigaba da bibiya dan ganin yadda za ta kaya idan wannan wakar ta fito.

Also Read

An yi wa maganar jarumi Momo mumunar fahimta a radiyo

 

An yi bikin zagayowar ranar haihuwar mawaki Umar M. Sharsef

Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Na Fara Film Ina Dan Wata Hudu a Duniya: Amude Booth

Leave your comment