An yi wa maganar jarumi Momo mumunar fahimta a radiyo

Photo Source: Burna Boy/Twitter

By Omar Ayuba Isah

Share On Whatsapp


Fittaccen jarumi a masana'antar Kannywwod, kuma mai shiryawa da gabatarwa a gidan talabishan na Arewa24 wato Aminu Sharif Momo ya yamutsa hazo a shafikan sada zumunta bayan da aka yi wa kalaman sa mumunar fahimta a hirar da ya yi a gidan radiyan Freedom da ke jihar Kano a ranar labara 10 ga watan feburerun 2021.

Jarumi Momo ya yi magana ne akan hanyoyin da za'a iya bi dan kawo gyara ga harkar finafinen Kannywwod da mutane ke cigaba da kuka da su akan su na taimakawa wajan gurbata tarbiyar al'umma. Momo a kalaman sa ya ce

Related News: Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

"Kai zakka ma da ake fitarwa, ya chanchanta ma adinga fitar da kudade daga cikin tsarin zakka, wadan da za a dinga shirye finafinai da fadakarwa da shiryeshirye domin jama'a su anfana. Daidai yake da ka gina masallatai da islamiyyu, gwara ka je ka bada kudin a yi shiryeshirye wadan da mutane za su dauki wa su darasi su anfana. A yanzu a yanayin da ake ciki, saboda tasirin yanzu illolin da ake ganin ana samarwa ta hanyar kallace kallace.

dan ka tura makudan kudade aka tsara finafinai da su, to za ka ga cewa yanzu yanzun nan ne sauyin zai samu. Idan har mutun zai bata awanni ko ya ki bacci ya na kallon shiryeshirye daga nan ya fada nan, ko daga wanchan group na WhatsApp ana turawa na nan, to idan aka cika su da shiryeshirye wadan da za su shiga ko ina to za a gani. Kuma ladan mutun sadakatul jariya ce, ko ina mutun zai tafi ya na nan har bayan rasuwar sa. Indai za a dauka a kalla, a gyara rayuwa a anfana a dauki wani darasi, to mutun zai samu lada".

Also Read

Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

Wannan su ne kalaman jarumin a cikin shirin " Barka da hantsi" na freedom radiyo da aka yi hira da shi tare da Afakallah shugaban tantance finafinai na Kannywwod. Sai dai da alamun mutane da dama ba su fahimci sakon jarumin a daidai ba, sai ake tunanin kamar ya nuna fifikon masana'antar Kannywwod ne akan masallatai da islamiyu.

Sai dai ma fi yawan ma su Allah wadai da jarumin ba wai sun ji abun da ya ce bane daga bakin sa, sai kawai daga shafikan sada zumunta ne su ka ga labarin na yawo su ma su ka bi yarima a sha kida.

Har yanzu dai jarumin bai ce komai ba akan batun kuma ana cigaba da tafka mahawara akan kalaman jarumin. Idan Momo ya ce wani abu akan batun, za mu sanar da ku akai.

Latest News

Watch Burna Boy Perform 'Onyeka' in New Video

6 New Naija Music Videos To Watch This Week

Burna Boy's "Destiny" In The US official Joe Biden Inauguration playlist (Video + Lyrics)

 Idols West Africa 2007 Winner Timi Dakolo Turns 40

 Burna Boy Presents 2020, Thankful And Hopeful For 2021 (Pictures)

 Top Naija Songs to Add to Your Valentine's Playlist

How Joeboy's Debut Album 'SBBM' Has Performed in First Week of Release

Teni ft Davido For You: Watch New Video Released

Leave your comment