Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

By Omar Ayuba

Send To A friend On Whatsapp

Duk da kasancewar wata biyu kachal yanzu da shiga sabuwar shekara ta 2021, amma alkalma da masana sun fara nuni tare da hasashen mawakan da ake ganin za su yi tashe a sabuwar shekaran nan daga Arewacin kasan nan.

Daga masana'antar Kannywwod ma dai hakan abun ta ke, duba da hasashen da masana da magioya bayan mawakan su ka yi, ana ganin a wannan shekarar da mu ke ciki, mawaka da dama ne za su yi tashe daga dukkan alamu, sabanin yadda a baya iya yan kalikan ne su ke kawai su ke tashe. Inda wani hasashe daga shafin Madubinaija ya wallafa sunayen wa su mawaka da ake ganin a sabuwar shekarar nan za su yi tashe sosai.

Mawakan dai wa su sun kwana biyu ana yayin su daman, inda kuma wa su sai a shekarar da ta gabata ne su ka fara tashe. Mawakan sun hadar da:


1- Hamisu Breaker

2- Auta MG boy

3- Ahmad Delta

4- Umar M. Shareef

 

Wadan nan su ne wa su daga cikin sunayen fitattun mawakan Kannywwod da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekaran nan ta 2021. Sai dai a gafe guda kuwa, akwai wadan da su ke ganin kamar zamani ya sauya da ba iya yan kalilan ne kawai za su ke tashe ba, domin yadda ake samun sabbin mawaka da jarumai akai akai wadan da su ke nuna bajintar su ta hanyoyi daban daban dan nishadantar da masoya.

Musanman yadda ba wuya yanzu abu zai yadu a kafafan sadarwa musanman na social media irin su Instagram, Twitter da Facebook har ma da YouTube.

Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Na Fara Film Ina Dan Wata Hudu a Duniya: Amude Booth

Ahmad Delta New Video to be Released

Teni ft Davido For You: Watch New Video Released

3 Best Joeboy Songs to Add to Your Valentine’s Playlist

Leave your comment