Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Photo Source: Lilin/Twitter

By Omar Ayuba

Send To A friend On Whatsapp

A kwanaki uku da su ka wuce ne fitaccen mawakin Hausa Hip Hop Lilin baba (on top), ya saki fefen bidiyan daya daga cikin wakokin da ya saki a cikin kundin wakoki da ya saki a wajan Jeneru data shige na shekakar 2021.

Wakar mai taken "Ahaiye" wace su ka yi ta tare da shima fitaccen mawaki kuma jarumi a masana'antar Kannywwod, wato Umar m. Sharef, ta ja hankali matuka tare da barin masoya da abun tafka mahawara a lokaci mai tsawo nan gaba, ganin yadda wakar ta kafa tarihin da ba a taba kafawa ba a masana'antar nishadi ta Arewacin Nigeria, na saka yan rawa har mutane chasa'in (90) a cikin bidiyan waka.

Lilin baba wanda ya saki kundin waka mai dauke da wakoki guda goma sha takwas (18) mai taken "Sounds from the north", ya kasance abun magana a yan kwanakin nan, duba da yadda ya ke cigaba da sakin wakoki kuma da bidiyan su babu kama kafar yaro. Gashi aiyukan da mawakin kai saki sun kai munzalin da za a iya saka su a jerin wakokin mawakan kudancin kasar nan da ma wa su daga nahiyar Afirika.

A cikin kudin na "Sound from the north", wa su daga cikin mawakan da Lilin baba ya gaiyata su ka yi waka tare a cikin kundin sun hadar da Umar m. Sharef, Adam A. Zango, Ali Isah Jita, Mister Bangis da dai sauran su. Mu na cigaba da bibiyan mawakin dan sanin yaushe ya ke shirya sakin wata kudin da wata majiya mai kusanci da mawakin ya sheda mana.

Kuma da zarar mun san halin da ake ciki, za mu sanar mu ku kai tsaye.

Leave your comment