Na Fara Film Ina Dan Wata Hudu a Duniya: Amude Booth

Photo Source: Amude/Twitter

By Omar Ayuba

Send To A friend On Whatsapp

Matashin jarumi kuma fitaccen yaron jarumi da aka yi a masana'antar Kannywwod shekaru da dama da su ka wuce wato Amude booth ya baiyana cewa tin ya na da watanni hudu kachal a duniya ne ya fara fitowa a finafinan Kannywwod.

Jarumin wanda kani ne ga shahararriyar jarumar nan ta Kannywwod da kuma Nollywood "Maryam Booth", kuma da ne ga tsohiwar jaruma kuma har yanzu a masana'antar ta Kannywwod wato Hajiya Zainab Booth, ya baiyana wa majiyar mu ce wa shi kan sa ba zai iya tuna sunan film din sa na farko ba, amma wa su daga cikin finafinan da zai iya tuna su da ya yi lokacin ya na dan yaro sun hadar da " Rashin uwa" da kuma "Azama".

Amude booth wanda yanzu haka ya fara tashe a matsayin makadi da kuma mawaki, ya kara baiyanawa majiyar mu cewa ya dauki kusan shekara biyar ya na koyan kida kafin ya fara yi wa mawaka aiki. Yaran jarumai dai da dama aka yi a masana'antar Kannywwod a shekarun baya, amma babu wanda ya kai Amude booth sanuwa a ma su shekarun sa kuma wadan da su shiga film a lokacin sa.

Wa su daga cikin sanannun jarumai yara sun hadar da dan gidan jarumi Ali Nuhu wato Ahmad Ali Nuhu, da dan gidan jarumi Ty shaban wato Sani shaban da kuma sauran su, idan aka cigaba da bin mu, za mu kawo mu ku sunayen yara jarumai da aka yi a masana'antar Kannywwod da kuma na yanzu sannu a hankali.

Leave your comment

Top stories

More News