Ahmad Delta New Video to be Released

Photo Source: Ahmad/Twitter

ByOmar Ayuba

Send To A friend On Whatsapp

Daya daga cikin fitattun mawakan Kannywwod kuma matashi wanda a yan kwanakin nan ne dai ya ke cigaba da daukan hankalin mutane da dama da irin salon wakokin sa na zamani wato "Ahmed Delta", ya shirya fitar da fefen bidiyan wakar sa mai suna "Rashin masoyi" a cikin watan nan da mu ke ciki.

Mawakin wanda mazaunin jihar Kano ne amma haihuwar jihar Delta da ke a kudancin kasan nan, kuma dan asalin kasar Niger, ya baiyana wa majiyar mu cewa, karbuwar wakar ce a cikin kankanin lokaci ne sa ya shi yanke hukuncin yi ma ta bidiyon wanda su ka yi aikin daukan jiya alhamis 10 ga watan feburerun 2021.

Wakar dai wanda fittacen mai bada umarni a kannywood wato Aminu S. Bono ya ba da umarnin dauka yayin da Nazifi kala ya yi aikin dauka, waka ce da ke nuni da yanayin da masoya su kan tsinci kan su a yayin da su ka rasa abar kaunar su ko ta hanyar rabuwa ko kuma ta Allah ta kasance wato mutuwa kenan.

Idan mai karatu zai tuna, a cikin wannan watan dai na feburerun nan ne mawakin ya saki sabuwar wakar sa mai suna "Duniya Labari", kuma tini wakar ta fara karade yanar gizo da kuma kafafan sada zumunci daban daban.

Musanman yadda masoya ke da rigerigen hawa kan wakar su ma ta fefen bidiyo dan nuna kaunar su ga mawakin da ma wakar. Ahmed Delta dai yana daya daga cikin mawakan da shafin Madubinaija ta wallafa su a matsayin mawaka goma da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekaran nan ta 2021.

Latest News

  Top 5 Trending Naija Songs That Should Not Miss On Your Playlist

New Music Round-Up - Nigeria: Ajebo Hustlers ft Omah Lay, Teni ft Davido, Chike ft Simi

Top Naija Songs to Add to Your Valentine's Playlist

How Joeboy's Debut Album 'SBBM' Has Performed in First Week of Release

3 Best Joeboy Songs to Add to Your Valentine’s Playlist

Valentines 2021: 5 Naija Songs to Dedicate to Your Partner

Leave your comment