An yi bikin zagayowar ranar haihuwar mawaki Umar M. Sharsef

Photo Source:GhLive

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp


A ranar alhamis din nan ne 10 ga wannan wakar ta feburerun 2021 ne, shahararren mawaki kuma jarumi a masana'antar Kannywwod Umar M. Shareef ya ke murnar zagayowar ranar haihuwar sa.

Jarumin ya wallafa wa su hotunan da ya dauka ne a shafin sa na Instagram da musalin karfe sha daya (11am) na yau juma'a, inda ya ke godiya ga yan uwa da abokan arziki da ma masoyan sa a bisa addu'oi da fatan alheri da su ka mai. Mawaki Umar M.

Shareef dan asalin jihar Kaduna wanda wakokin sa su ka karade ko ina a arewacin Nigeria da ma wa su kasashen indai hausawa ke da zama ya na cigaba da bunkasa a fagen wakokin zamani da harshen hausa, musanman idan aka yi duba da sabin aiyukan da ya ke saki a yan shekarun nan.

Ko a yan kwanakin nan ma jarumin kuma mawaki ya saki sabuwar bidiyon wakar sa mai take "Wa zana bawa kai na" inda hallau dai ya sake fitowa a wakar su da Lilin baba a satin nan mai taken "Ahaiye". Mawaka da jarumai da dama ne su ka halacci bikin zagayowar ranar haihuwar ta sa. Daga nan mu ma mu na wa Umar M. Shareef fatan alheri da karin shekaru ma su albarka.

Latest News

Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

 

Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Na Fara Film Ina Dan Wata Hudu a Duniya: Amude Booth

Teni ft Davido For You: Watch New Video Released

Okyeame Kwame Says His Son is not like Him

Leave your comment