Yakubu Muhammad New Series Release

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Babban jarumi kuma mawaki sannan marubuci hadi da bada umarni a masana'antar shirye finafinai ta kannywood, Yukubu Muhammad ya yi sanarwa ta musanman dangane da sabuwar film din da su ke shirin saki a sabuwar wata mai kamawa ta March na 2021.

Film din mai dogon zango da aka wa taken "Gidan Danger" zai fito ne ranar 1 ga watan 3, na shekarar nan da mu ke ciki da musalin karfe 8 na dare a tasher TSTV da kuma tasher su ta YouTube. Film din dai wanda Sani Danja ya shirya shi kuma Yakubu Muhammad ya ba da unarni, film ne da aka dauke tsawan lokaci ana daukan sa tare da kuma maganganu akai.

A karkashin 2effect production wanda mallakan shahararrun jaruman biyu ne ake shirya wannan film mai dogon zango da ke dauke da fuskokin manya da kuma kananan jarumai a Kannywood. Tin bayan wannan sanar war ne, masoyan su su ke cigaba da baiyana ra'ayin su akan wannan sabuwar film da zai fito kwanaki goma sha shida (16) ma su zuwa.

Kimanin sama da mutun miliyan daya ne ke bin jarumi Yakubu Muhammad a shafin sa na Instagram kuma tini kwanfanin na Instagram ta sheda shafin mawakin a matsayin ingantacen shafi kuma mallakar mawakin ne ba na bogi ba. Jaruman biyu dai abokai ne shekara da shekaru, kuma duk kannin su jakafun kwanfanin sadarwa ne na Glo shekara da shekaru.

Sannan sanannu ne a masana'antar finafinai ta Nollywood da ke kudancin Nigeria, abotar su dai ta yi jumawar da masoya sun ma daina ganin su a matsayin abokai sai dai yan uwa. Kuma har yanzu abotar gaba take yi ba alamun baya.

Muna fatan jarumai da abokai ne ko kawaye za su yi koyi su ma da wadan nan manyan mawakan da su ka rike abotar su ta shekaru ma su yawa.

Also Read

News on Namenj and Hamisu Breaker new song

An yi wa maganar jarumi Momo mumunar fahimta a radiyo

An yi bikin zagayowar ranar haihuwar mawaki Umar M. Sharsef

Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Na Fara Film Ina Dan Wata Hudu a Duniya: Amude Booth

Leave your comment