Bayan danben kece raini, Madox da 442 sun yi sulhu a tsakanin su har sun fitar da sabuwar waka tare.

Photo source: Madox and 442's Instagram highlights)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

"Zo mu zauna zo mu saba", a wani karin maganar bahaushe, " Idan kowa ya yadda da ajizancin sa, sai a yafi juna a cigaba da zaman tare" a cewar wani marubucin Kalamai ga zuci.

A satin da ta gabata ne duniyar mawakan Hausa Hip Hop ta wayi gari da labarin rigimar da wasu matasan mawakan ta biyu su ka yi a wani hotel da ke garin Kaduna, wato Madox tbb dan jihar Kano da kuma Mr 442 dan garin Zaria da ke Kaduna. Wanda wannan fadan shi ne fada na farko a tarihin masana'antar da ya kai ga dambe a tsakanin mawaka biyu kuma hakan ya fito fili ta fefen bidiyo.

Amma abun da ya fi wannan damben na su bada mamaki sh ne labarin shiryawar su a cikin kwanaki uku kachal bayan fadan na su. Tin a shekaran jiya asabar 6 ga watan 3 na 2021 ne, aka ga mawaki Madox ya na ta daura hotunan Mr 442 abokin fadan na sa tare da sanarwa cewa akwai albishir na wani abu da zai fito daga su biyun. Wanda hakan ya sa masoyan sa cikin rudani, sai gashi jiya lahadi mawakin ya cire su daga cikin wannan rudanin a yayin da ya fitar da hoton wani waka da ke dauke da hoton shi da 442 mai suna "Sai Monday".

Also Read: Namenj ya fitar da sabuwar wakar sa tare da Hamisu Breaker

Ya kuma baiyana cewa wannan wakar ta sa tare da Mr 442 mai suna "Sai Monday", zai fito ne ranar Monday, wato yau kenan. Kuma tini wakar ta fito a shafuka daban daban da man'hajojin sauke wakoki irin su Audiomack wanda tini wakar ta samu sama da mutane dubu baya su ka saurarin wakar daga fitowar ta yau din nan. Daman ita zaman lafiya ta fi zama dan sarki, kuma ita rayuwar mawaki nadubi ne ga matane da dama, dan haka fada ko gaba ba abun yi ba ne ga mawaki ko duk wani mai daukaka.

Latest News

Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.

 Makadin jita da hannaye biyu David Swauzo ya fitar da sabuwar waka bayan dawowar sa Najeriya.

Isah Ayagi ya fara tallata sabon kundin sa.

Abun da ya sa wakokin Hausa ba sa sanu a duniya kamar na ragowan wakokin kudu ba

Download Hausa Music:Top 5 Artists; Umar M. Shariff, Nura M. Inuwa, Isah Ayagi, Hamisu Breaker, Adamu Hassan Nagudu… (FREE Download)

Feezy ya saki bidiyo daya a cikin kundin sa ta Kingdom.

Leave your comment