Abun da ya sa wakokin Hausa ba sa sanu a duniya kamar na ragowan wakokin kudu ba

Join Us on Telegram


Babu tantama wakokin Hausa na daya daga cikin manyan wakoki a nahiyar Afirika, sautin ta da salon ta sananne ne a kunnuwar masu jin waka domin ba ta sauya daga tsarin ta na asali ba wato gargajiya da al'adar kabilar Hausa. Dan haka wakokin Hausa ga kunnuwan bakon mutun, na iya fadawa rukunin sanannun salon wakoki na nahiyar Afirika irin su Taarab, Amharic, Rhumba ku kuma Afro beat wanda mu ka fi sani da salon Fela. Wasu tsiraru daga cikin mawaka sun yi namijin kokari dan ganin sun kai darajar wakokin Hausa sama kuma su yi gogaiya da ragowar wakoki sanannu a duniya irin su Hip Hop (Gambayar zamani) da R & B (rerarriyar waka cikin sanyin murya).

Also Read:Yaron matashin mawaki Freiiboi shaban zai fitar da sabuwar waka kwanan nan.

A nazartar dalilan da ya sanya wakokin Hausa ba su sanu sosai a duniya ba, wasu masana wakokin da mawakan Hausan sun baiyana mai su ke ganin ya haddasa wannan koma baya da wakokin Hausa ke fama da shi a duniya, kuma ga wasu daga cikin dalilan da su ka baiyana nan a kasa kamar haka:

Girman kai wajan wakar hadaka da wasu mawakan, an sheda cewa mafi yawancin mawakan Hausa ba sa waka da sanannun mawaka daga wasu sassan har da wadan da ma ba a yanki daya su ke ba a kasar ko kuma nahiyar su ce ba daya ba. Wani lokacin da gangan su ke kin wakar da su dan kada su sauya su daga yadda su ka sama waka a al'adance ko dan kada asalin salo da sautin da aka san wakokin Hausa da su su sauya a dalilin waka tare da wasu mawakan da ba hausawa ko yan kasar Hausa ba. Wani lokacin kuma girman kai da ji da kai ne ke hana su neman wadan nan mawaka na wa su yankin ko shiya ko kasa dan su yi wakar tare. Har yanzu ba mu da takamemen dalilin kin yin waka da wasu sanannun mawakan a duniya dan daga darajar wakar Hausa a sanadiyar hakan. Amma wajibi ne mu yadda cewa wakar hadaka hanya ce mai sauki wajan kaiwa ga sababbin mutanan da ba su san ka ko wakar ka ba cikin sauki tare da karya iyakar da al'ada kan iya gindayawa idan har ba a yi wakar hadakar ba da wasu. A duk lokacin da mawaka su ka yi wakar hadaka, masoyan su za su saurari wakar ne saboda kaunar da su ke wa gwanin su da ke cikin wakar, yayin da hakan zai sa su saurari dayan mawakin ko mawakan saboda kara tinda na su gwanin shima ya na cikin wakar. Wanda hakan babbar dama ce ga masoya wajan sanin wasu mawakan da ba su sani ba balle su yi sha'awar jin wakokin su.

Too Proud to Collaborate? 

 

 

Hausa to the world, they will not know what hit them. 

 Rashin tafiya da zamani, masana nazartar wakokin Najeriya da dama sun nuna damuwar su bisa yadda mafi yawanci mawakan Hausa ba sa tafiya da zamani ko yunkurin cigaba ko sauya yadda su ke gudanar da wakokin Hausa, dan ta yi gogaiya da sauran wakoki da ake yi a kudancin Najeriya da harshen Tarabanci, Inyamaranci, Turancin Pidgin da ita kanta Turancin ta ainahi. Mawakan Hausa sun shagala da yin waka da iya harshen su ta Hausa ba tare da yunkurin hadawa da wa su yararrukan da mu ka ambata a baya dan wakar da shiga wasu guraran kuma su jiyu a dalilin wadan nan yararrukan da ake da hadawa a ciki. Ga shi da yawan su idan su ka yi bodiyo ba sa fassarawa a rubuce mai ake fada a cikin wakar kamar yadda mawakan wasu kasashen da ba a jin yaran su ke yi a kasan bidiyan su irin su Diamond Platnumz dan kasar Tanzania wanda abun daurewar kan shine yadda shi yawancin mawakan Hausa ma su salon Nanaye ke kwafa a waka. Rashin wannan tafiya da zamanin ya janyo tsayawar wakokin Hausa guri daya kuma ga iya majiyan yaran Hausan kawai wakokin ke kaiwa, sabanin yadda na wasu yararrukan ke shigowa kasashen hausawan irin su wakokin Diamond da mu ka yi musali da shi a baya.

Babu kwamfanunnuwan kula da mawaki (Record Label), da na kasuwancin wakokin hade da dabarun kasuwancin wakokin. Ingantattun kwanfanunnuwa ma su tsari irin na zamani wajan lura, kula da kuma gogar da mawaka da kuma wadan da su ka kware wajan cinikaiyar wakokin Hausa ga sauran duniya kamar yadda ake yi a ko ina, kusan abu ne da za'a ce duk yankin hausawa babu ko da kwaya daya tsayayye cikakke mai kuma aiki yadda ya kamata. Ko da kuwa akwai, toh na jeka na yi ka ne. Wannan kenan na nifin wakokin Hausa ba sa kaiwa lungu da sakon da ya dace ya kai, sannan hakan ya janyo rashin wani tsari ingantace tabbatacce wajan tsara kasuwancin mawaka da wakokin su.

Shi kasuwancin mawaka da wakokin su jigo ne a cigaban mawaki da ita kanta harshen da ya ke waka da ita musanman ga mutanan da ba su saba da jin salo da wannan yaren ba na mawakin.&

Leave your comment