Yaron matashin mawaki Freiiboi shaban zai fitar da sabuwar waka kwanan nan.

Photo source: TY Shabaans Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Shahararren matashin mawaki kuma da' ga fitaccen mawakin nan kuma Jarumi TY Shaban wato "Freiiboi shaban" ya shirya sakin sabon bidiyan sa mai suna "Kalangu" a kwanan nan. Wannan sanarwar ta fito ne daga mahaifin sa ta shafin sa na Instagram jiya laraba da yanma.

Tini aka riga aka yi aikin wannan bidiyan kuma a sanarwar da mahaifin ya fitar, ya nuna cewa ba da jumawa ba wannan bidiyan zai fito ga masoyan dan na sa. Freiiboy wanda daya ne daga sanannun kananan yara ma su waka a salon Hausa Hip Hop da Afro Pop a Arewacin Najeriya kuma daga jihar Kano, ya fara waka ne a shekarun baya kusan lokaci daya da irin su marigayi Lil Amir da kuma dan gidan fitaccen mawakin nan kuma jagora "Billy-O", wato Hanny Billy-O da irin su Lil Abdul, MMTee da sauran su.

Also Read: M-kay zai fitar da fefen bidiyon sa ranar 5 ga watan nan


Haka zalika Freiiboi shaba na daga cikin mawakan yara da su ka gaji waka daga iyayen su, inda mahaifin sa TY shaban mawaki ne sanannan a shekarun baya, kamar Hanny Billy-O da shima da' ne ga Billy-O. Sannan Freiiboi na daga cikin mawakan yara da su ke da tarin wakoki kuma bidiyo da dama wanda su ka kai munzakin da za su iya karawa da mawaka da dama a duniyar mawaka.

Masana da dama na ganin kokarin da mahaifin sa ke cigaba da yi akan yaron ne ya yi sanadiyar sanuwar sa cikin kankanin lokaci, kuma ana ganin idan hakan ya cigaba da kasancewa, to babu makawa shaharar Freiiboi zai fi yadda take a halin yanzu.

Wasu daga cikin makadan da su ka yi wa Freiiboi aiki sun hadar da irin su Mega Mix, Don Adah, Sonikman, Nexcezz Beatz, Kefazz, Mujahid Duma da dai sauran su, mawaka kuwa da ya yi aiki da su akwai irin su Hanny Billy-O, Bmeri Aboki, Dr pure, Mighty, Eddy Kool da dai sauran su.

Top Stories

Burna Boy Featured in Justin Bieber's Upcoming Album 'Justice'

Top Trending New Naija Music Videos to Watch This Week

Latest Sinach Songs: Sinach Drops New Song 'Beautiful' Featuring Nathaniel Bassey

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Download Rema: Another Banger! ‘Bounce’, Rema Releases New Song (LYRICS)

Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

Leave your comment