Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

Photo source: from Hussaini Danko's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Mawaki Husaini Dango na shirin sakin sabuwar waka a kwanan nan, mawakin ne ya baiyana hakan bayan da ya daura fefen bidiyo na makadi Kashepu a yayin da ya ke sauraron wakar ta sa a cikin studio din kashepun inda aka yi aikin wakar daga dukkan alamu.

Husaini Danko wanda a yan kwanakin kaya ne ya fitar da wakar Maryam wacce ta ke cigaba da jan hankalin masoya wakokin sa. Duk da dai wannan sabuwar wakar Husaini Danko din bai ma ta suna ba ko sanarwa ranar da zata fita. Amma akwai yuwar mawakin na hada wakokin da zai fitar da su ne a kundi cikin shekarar nan, ganin duk shekara daman mawakin kan firar da sabuwar kundin wakoki a kasuwa.

Za mu iya cewa mawaki Husaini Danko na daya daga cikin manyan mawaka da su ka juma wakokin su na samun karbuwa a gun masoya da kuma hausawa musanman mazauna garuruwan kudu. Kuma akwai tarin finafinai da mawakin ya yi wakokin cikin fin din da kuma wasu wakoki na hadaka na manyan mawaka a masana'antar Kannywood.

Sama da masoya mutun dubu dari biyu ne da wani abu su ke bin mawakin a shafin sa na Instagram.

Labarai da dumidumin su

Ahmad Delta ya shirya fitar da bidiyan wakar Rashin masoyi.

 

Grafix designer KG ya angwance

Mawaki Feezy ya wallafa sunayen wakokin da ke cikin sabuwar kudin sa

Matashin mawaki YK Designer ya saki sabuwar fefen bidiyo mai tsarin zamanin da.

Thanks Masoya sun shiryawa Fresh Emir walima ta musanman a jihar Kano

Mawaki M-kay ya yi bidiyan wakar "Nobody" a garin Abuja

Leave your comment