Ahmad Delta ya shirya fitar da bidiyan wakar Rashin masoyi.

Photo source: from (Ahmad Delta's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Daya daga cikin manyan matasan mawaka a masana'antar Kannywood wato Ahmad Delta ya shirya fitar da fefen bidiyan wakar sa mai taken "Rashin masoyo" a ranar lahadin nan mai zuwa ta 28 ga watan 2 na 2021.

Mawakin ya baiyana hakan ne bayan da ya saki dan gajeran fefen bidiyo a matsayin taba ka lashe da kuma albishir daga cikin bidiyan wakar ta sa wacce zai saki a ranar lahadin.

Ahmad Delta ya baiyana wa wakilin Madubi Naija ta shafin WhatsApp cewa wakar za ta fita da misalin karfe 12 na rana a YouTube da kuma sauran kafafen sadarwa na yanar gizo. Mawakin ya cigaba da baiyana wa wakilin Madubi Naija cewa, Directa Aminu S. Bono ne ya bada umarnin aikin kuma zai fito ne a karkashin kwanfanin directan mai suna "Bono Movies".

Makadin zamani mai kuma tashe a halin yanzu "Kashepu" ne ya yi aikin audio din wakar, yayin da matashiyar jaruma Bilkisu Salis ta fito a cikin fefen bidiyan. Nazifi kala ne ya dauki bidiyan a yayin da Ameer Editor ya yi aikin editing.

Ahmad Delta na cigaba da karbuwa a zukatan masoya wakokin rauji wato Nanaye da kuma masoya finafinan kannywood. Inda ake ganin mawakin ya zo da salo na daban kuma da alamun a shekarar nan zai ba da mamaki sosai a masana'antar.

Har yanzu wakar Ahmad Delta ta "Duniya labari" da ya saki a kwanan nan ne ke cigaba da samun shiga a gun mutane da dama musanman wadan da ba su san mawaki Ahmad Delta ba a baya.

Labarai da dumidumin su

Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

 Grafix designer KG ya angwance

Mawaki Feezy ya wallafa sunayen wakokin da ke cikin sabuwar kudin sa

Matashin mawaki YK Designer ya saki sabuwar fefen bidiyo mai tsarin zamanin da.

Thanks Masoya sun shiryawa Fresh Emir walima ta musanman a jihar Kano

Mawaki M-kay ya yi bidiyan wakar "Nobody" a garin Abuja

Leave your comment