Mawaki M-kay ya yi bidiyan wakar "Nobody" a garin Abuja

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Shaharren mawakin Hausa Hip Hop, R & B, Reggae da kuma Afro pop, wato "M-kay" (Arziki) ya yi bidiyan sabuwar wakar sa mai suna "Nobody" a garin Abuja babban birnin taraiyar Nigeria.

A ranar daya ga watan nan ne na feburerun 2021 M-kay ya saki wakar "Nobody" a matsayin wakar sa ta farko a sabuwar shekarar nan, wakar wanda ta samu karbuwa a gun yan mata da dama tin a satin farko na fitowar ta, waka ce ta soyayya da ke da salon kida irin na kasar Afirika ta kudu (South Africa) da kuma kalamai ma su shiga ran masoya.

 

M-kay, daya ne daga cikin manyan mawaka a masana'antar Hausa Hip Hop, kuma daya daga cikin na hannun daman fitaccen mawaki "Billy-O" inda tin a shekarar 2009 ne mawakin ya fitar da wani kundin bidiyo na salon wakar rauji wato (Nanaye).

Tin bayan nan mawakin ya yi fittattun wakoki irin su:
Sauti original, in zaki so ni, Arewa mama, Talatu, Blessings da kuma Zainabu wacce su ka yi tare da Uniquepikin da kuma Dabo Daprof (Mister Ladagoma). Wannan sabon bidiyo da aka dauka a garin Abuja ya ja hankalin masoyan mawakin dan ganin irin kayan aikin da ake daukan wannan bidiyo da shi.

Fatan mu dai anan shi ne mawaka su cigaba da kokartawa wajan ganin sun yi wa wakokin su bidiyo da zarar audio ta fito, domin duniya yanzu ga kallo ta fi karkata kafin saurara ya biyo baya.

Leave your comment