Grafix designer KG ya angwance

Photo source: from (KG's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Sanannan mai grafix design kuma mai bada umarni tare da editing na bidiyo dan asalin jihar Kano Khalifa Yau Usman da aka fi sani da suna "KG" wato Khalifa Grafix, ya ankwance a ranar asabar 20 ga watan 2, na shekarar 2021 a jihar sokoto birnin shehu.

An daura auran KG din ne tare da amaryar sa Bilkisu Haruna Ibrahim a gidan Malam Ibrahim mai kasuwa dake ungwar Dan marke a jihar sokoto da misalin karfe 10 na safe. KG ya wallafa hotuna daga wajan bikin ga abokai da yan uwa da ba su samu daman halattar bikin ba, ta shafin sa na Instagram.

Inda wa su daga cikin manyan mawaka irin su Bello Vocal su ka daura hoton KG din tare da masa fatan zaman lafiya a auran. KG dai kafin ya bada karfin sa ga daukan fefen bidiyo da kuma sarrafa na'uwar drone (wato kemeran nan mai kama da jirgin sama), an fi sanin KG ne a harkar Grafix Design, Artwork na waka, kundi da kuma fastan finafinai na kannywood.

Wasu daga cikin mawakan da KG ya yi aiyukan grafix a baya sun hadar da Ali Jita, Ado Gwanja, Aji Karrowz, Nexcezz Beatz da dai sauran su, a fanin bidiyo kuwa, akwai manyan mawaka irin su Morel, Ali Jita, Classiq da dai sauran su.

Khalifa dai na daya daga cikin grafix designer da su ka fito dsga jihar Kano kuma ake alfahari da su a fanin bidiyo grafix da kuma sarrafa na'uran nan ta drone wato kemera mai kama da jirgin sama.

 

Labarai da dumidumin su

Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

Ahmad Delta ya shirya fitar da bidiyan wakar Rashin masoyi.

Mawaki Feezy ya wallafa sunayen wakokin da ke cikin sabuwar kudin sa

Matashin mawaki YK Designer ya saki sabuwar fefen bidiyo mai tsarin zamanin da.

Thanks Masoya sun shiryawa Fresh Emir walima ta musanman a jihar Kano

Mawaki M-kay ya yi bidiyan wakar "Nobody" a garin Abuja

Leave your comment