Mawaki Feezy ya wallafa sunayen wakokin da ke cikin sabuwar kudin sa

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Kani ga Dj Ab kuma daya daga cikin manyan matasan mawaka a arewacin Nigeria wato "Feezy" ya saki sanarwar sunayan wakokin da ke cikin sabuwar kundin sa mai taken "Kingdom", wacce mawakin ke shirin fitar da shi nan ba da jumawa ba.

Kundin wanda ya ke kunshe da wakoki guda hudu kamar yadda Feezy ya baiyana a kwanakin baya, ya na dauke ne da wakoki uku da Feezy kadai ya raira su wadan da su ka hadar da "Kingdom" a matsayin waka da farko kuma sunan kundin kenan, sai wakar "Crime" a matsayin waka ta uku a kundin sai kuma wakar "Mai ya rage" ta matsayin waka ta kudu kuma ta karshe a cikin kuundin.

Waka ta biyu ce kawai wakar da Feezy su ka yi ta tare da wani wato wakar "Baby na" tare da "Marcay". Daga duk kan alamu wannan kundin zai fito nan ba da jumawa ba domin alamu sun nuna cewa mawakin ya kammala aikin wannan kundi, kuma sakin ta ne kawai ya rage.

Feezy ne da kan sa ya rubuta wakokin tare da aikin su gabaki daya kuma zai saki kundin ne a karkashin kwanfanin " Wonderwise productions".

Leave your comment