Matashin mawaki YK Designer ya saki sabuwar fefen bidiyo mai tsarin zamanin da.

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Fasihin matashin mawaki, mai bada umarnin bidiyo, mai zanen animation da kuma grafix designer "YK Designer" ya saki sabuwar fefen bidiyo mai tsarin zamanin da a cikin watan nan da mu ke ciki. Mawakin wanda a kwanan bayan nan ne ya fitar da wakar "A sa mana ganga" wacce bidiyan ta ke cigaba da samun karbuwa tin bayan da ya fito a cikin shirin zafafa goma na tashar Arewa24, wacce Nomiss Gee ke gabatar da shi.

Ya sake sakin sabuwar waka mai suna "Asha rawa", hade da fefen bidiyo mai daukan hankali. Salon bidiyon ya ja hankali sosai tare da janyo mawahawa a tsakanin masoya da dama har ma da wa su mawakan, inda kowa ke tofa albarkacin bakin sa dangane da irin yadda fefen bidiyan ya fito da wani salo irin na zamanin da.

Kama daga kayan da aka saka, inda aka yi bidiyan, irin aikin da aka yi na editing da kuma labarin da a ka nuna a cikin fefen. YK Designer dai dan asalin jihar Kogi ne amma haihuwar jihar kano kuma girman kano. A halin yanzu wannan wakar na kan manhajoji da dama manya manya kuma haka fefen bidiyan shi ma ya ke kara shiga mutane inda mutane ke cigaba da tofa albarkacin bakin su a kan wannan aikin.

Tin bayan kammala karatun sa a jamiyar Bayero da ke Kano in da ya karanci "Agric" da kuma bautar kasa wato " Youth service) a jihar Jigawa, YK Designer ya shiga harkar waka gadangadan da kuma harkar hoto. YK Designer na daga cikin matasan mawakan da shafin "Madubi Naija" su ka wallafa sunayen su a matsayin mawakan da ake sa ran za su nuna bajinta a sabuwar shekara ta 2021.

Leave your comment