Thanks Masoya sun shiryawa Fresh Emir walima ta musanman a jihar Kano

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Mawakin Hausa Hip Hop wanda salon wakokin sa su ka samu karbuwa a cikin al'umma a yan shekarun nan wato Fresh Emir (Aku mai bakin magana) ya samu kauna ta musanman a gurin wa su daga cikin masoyan sa, in da su ka hada mai walima ta musanman tare da gaiyato shi wajan waliman dan nuna mai irin ta su gudunmawar.

Mawakin wanda ya wallafa wa su gajerun bidiyoyi guda uku a shafin sa na Instagram, ya baiyana farin cikin sa ga wadan nan masoyan na sa tare da jinjina mu su akan wannan karamci da su ka yi mai.

Fresh Emir wanda shi ma na daga cikin mawaka goma (10) da shafin "Madubi Naija" ta baiyana su a matsayin mawakan da ake sa ran za su nuna bajinta a sabuwar shekara ta 2021, daya ne daga cikin bloggers din nan ma su wannan shafin na Hausatop da kuma Hausatop TV tare da abokin sa kuma yanzu manajan sa wato "Mus'ab Sadauki" wanda shi ma a halin yanzu ya zama mai bada umarni da kuma shiryawa.

 

Fresh Emir kafin fara wakokin fadamarwa da janhankali na "A yau" series, tare su ke waka da abokin na sa wato "Mus'ab", wanda ya koma manajan fresh emir bayan an fara series din " A yau". Tin dai bayan sakin wasiga ga shugaban kasa na biyu da Fresh Emir ya yi, har yanzu bai fito da wani sabon aiki ba, amma akwai alamun mawakin ya na shirya wa su abubuwa ne a boye.

To koma ya abuj yake, mu anan sai dai mu ce jinjina ga masoyan Fresh Emir kuma fatan zai fito da sabuwar waka a farkon watan nan da za mu shiga ko tsakiyar ta.

Leave your comment