Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Photo source: Billy's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Jigo, uba kuma babba a masana'antar Hausa Hip Hop Alhaji Bello Ibrahim wanda duniya ta fi sani da suna "Billy-O" ya saki sabuwar bidiyo din wakar sa mai suna "Ina son ki" wacce amshin wakar an ara ne daga cikin wakar babban mawaki "Sadi sidi sharifai" wanda ya yi a shekarun baya.


Billy-O ya yi wakar ne a shekarar da ta gabata ta 2020 inda kuma wakar ta samu karbuwa matuka a cikin Arewacin Najeriya, wanda watakila hakan na da nasaba da bidiyon da ya biyo bayan nasarar wakar. Domin rabon da shahararren mawakin kuma malamin turanci a makarantar koyan turanci ta "Jammaje Academy" da kuma ma'aikaci radio a Dala Fm 88.5 Kano, ya yi bidiyan waka tin wakar "Lamarin ne bambam", wanda makadi A-styl ya yi aikin wakar.


Billy-o wanda mahaifi ne ga daya daga cikin yaran mawakan Hausa Hip Hop wato Hanny Billy-O, na daga cikin manyan mawakan Hausa Hip Hop da duniya ke ganin har yanzu ba a yi kamar su ba a fannin shura da wakoki ma su nisan tashe kuma daya daga cikin mutanan da su ka yi yaki cikin lumana ta hanyar anfani da radio wajan kira ga matasa kan tsaftace harshe da kuma neman ilimi da sana'ar dogaro da kai.


Wannan fefen bidiyo ya fita ne babu wata sanarwa ta hannun mawakin da kan sa a shafin YouTube tare da baiyanawa majiyar mu cewa bidiyon da zai fitar nan gaba shi ne bidiyon wakar sa ta " Jamila".

"Sarki Billy", kamar yadda mafi yawan mawakan Hausa Hip Hop da Masoya ke masa lakabi, ya bada gudunmawa a fannoni daban daban tare da zamowa silar shigar dubunnan mawaka cikin Hausa Hip Hop irin su Dj Ab, B.O.C, Classiq, Bmeri Aboki, da dai sauran su.

Leave your comment