M-kay zai fitar da fefen bidiyon sa ranar 5 ga watan nan

(photo credit: from M-kay's official Instagram page)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Sanannan mawaki kuma kwararren mai daukan hoto "M-kay" ya shirya tsaf dan fitar da sabuwar fefen bidiyan wakar "Nobody" a ranar biyar ga watan uku shekarar 2021 idan Allah ya kaimu. Wannan sanarwar ta fito ne daga mawakin da kan sa ta shafikan sa na Instagram da Facebook, a jiya talata. Inda ya yi masoyan sa albishir da fitowar wannan wakar a ranar juma'a din nan mai zuwa, sai dai bai sanar da hakikanin karfe nawa ba wakar zai fito.

Idan ba'a manta ba, a ranar 1 ga watan biyu ne na shekarar 2021, M-kay ya saki audio din wakar "Nobody" a shafukan sada zumunta. Wanda a cikin kwanaki uku kachal ne yan mata sama da hamsin (50) su ka dinga yi wa wakar bidiyo challenge a shafukan su. Wanda hakan ya sanya mawakin zuwa jihar Abuja dan yin aikin bidiyon wakar, inda kwararran mai bada umarnin nan Ahmadi ya yi aikin bidiyan.

Also Read: Nazifi Asnanic ya fitar da sabuwar wakar sa


M-kay wanda daya ne daga makusantan shahararan jagoran Hausa Hip Hop Billy-O, mawaki ne mai salon wakokin Rap, R & B, Reggae da ma salon Rauji wato nanaye idan ya so. Har izuwa yanzu tin bayan kammala aikin bidiyan, M-kay na cigaba da zama a garin na Abuja tin barin sa jihar sa na asali wato jihar Kano.

Masoyan sa su na cigaba da baiyana farin cikin su da wannan albishi tare da baiyana ra'ayin su akan yadda bidiyan ya kamata ta kasance idan ta fito. Wakar "Zainabu" ita ce wakar M-kay ta karshe a shekarar da mu ka yi bankwana da shi, wace su ka yi tare da Mister Ladagoma da kuma Uniquepikin. M-kay na daga cikin mawakan da ba su fiye sakin wakoki da yawa ba sai dai jifa jifa, amma kuma su kan juma ana yayin su idan ya fitar.

Latest News

Mawakan Hausa Hip Hop sun dambatu a wani hotel

Yan Kannywood sun shirya wasan kwallon kafa a madadin dan uwa a masana'antar; Musty Dan ko

Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment