Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Photo source: Umar's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel


Sanannan mawaki, makadi kuma jarumi a masana'antar Kannywood Umar M. Shareef ya saki sabuwar waka mai suna "Lagwada" a ranar lahadi 28, ga watan faburerun shekarar 2021.

Wakar "Lagwada" wanda fitaccen mawaki kuma makadi a legas wato "Selebobo" ya yi aikin sa, ta fita ne a daidai lokacin da mawaki Umar M. Shareef ke cigaba da samun yabo daga dubunnan masoya akan irin sabon salon da mawakin ya koma rera wakokin sa tare da fefen bidiyoyin sa.

Also Read: Mawakiya Jamila "Jamcy" ta saki sabuwar bidiyan wakar ta

Mawaki Umar M. Shareef dan asalin jihar Kaduna, a wannan sabuwar shekarar ya nuna alamun zai juma ya na tashe a masana'antar Kannywood da na wakar Rauji wato "Nanaye". Lagwada daga sunan, waka ce da sunan ke nuna alamun ta rawa ce da chashiya. Amma sai mai sauraro ya saurara sannan zai gane ko wani irin waka ce.

Umar M. Shareef ya wallafa sanarwar ne a shafin sa na Instagram a ran lahadi da ta zo daidai da rana ta karshe a watan biyu ga shekarar nan ta 2021. Kuma masoyan sa da dama ne su ka fara baiyana ra'ayin su akan wakar da mawakin ya fitar, kuma an sa ido akan wani irin bidiyo mawakin zai fitar idan ya tashi fitarwa.

Latest News

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 

Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment