Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Photo source:Mixterbash's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop makadi kuma ma'aikaci a gidan radio ta talabijan "Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan nan mai kamawa ta March a yanar gizo.

Mawakin ya sanar da haka ne jiya alhamis 25 ga watan 2, ta shekarar 2021 a shafin sa na Instagram karkashin wani hoto da ya wallafa wanda shi da shahararren mawaki " Hamisu Breaker su ka dauka tare a birnin taraiya Abuja.

Inda ya baiyana cewa gidan radio din sa ta yanar gizo wato (online radio) mai suna "Sautizallah" zai fara aiki a watan March kuma kofa a bude take ga duk wani mai son ya yi hadin gwiwa ko taraiya da shi dan gudanar da gidan radio din wacce ta samu sunan da daga shafin yanar gizo ta mawakin mai suna "Sautizallah.com wanda aka fara shi a yan shekaru da su ka wuce. Mawaki Mixterbash wanda ma'aikaci ne a gidan radio na BBC tin bayan barin sa aiki a gidan radiyan Kano Fm da kuma gidan TV na farin wata. A karshen shekaran nan da ta muce ne mawakin ya angwance a garin Kano inda a nan mawakin ya shahara a masana'antar Hausa Hip Hop.

Leave your comment