Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Photo source: Sonikman's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Makadi,mawaki, mai zane da kuma director a masana'antar Hausa Hip Hop da Kannywood wato Sani Suleiman da aka fi sani da "Sonikman" ya saki sabuwar wakar sa mai suna "Mama Yeah", wacce ya yi tare da mawaki Slim B da kuma A-styl, wanda dukkan nin su manyan makada ne kuma mawaka.

Mawakin ya saki sabuwar wakar ne jiya a shafukan sa na Instagram da Facebook. Inda kuma ya saki wakar da wani fefen bidiyo na cartoon. An yi wakar a shekarar da ta gabata ne a lokacin da Slim B ya shigo Nigeria daga kasar Niger in da yanzu mawakin dan asalin Nigeria ke da zama yanzu.

Sai dai tin a wanchan lokacin masoya da dama su ke dakon fitowar wannan wakar, amma sai a wannan watan da mu ke bankwana da ita na feburerun 2021 ne mawakin ya saki wakar ba tare da tsanmani ko sanarwa ba.

Sonikman ya na daya daga cikin manyan mawaka daga jihar Kano wanda su ke kan gaba a wakokin salon R & B da Afro pop, kuma ya bada umarnin bidiyo da dama a takwayen masana'antun Hausa Hip Hop da Kannywood. Ana ganin wannan sabuwar wakar za ta samu kwararran bidiyo daga mawakan dan ganin cewa Sonikman da Slim B duk kannin su ma su bada umarnin bidiyo ne tare da editing.

Leave your comment