Mawakiya Jamila "Jamcy" ta saki sabuwar bidiyan wakar ta

Photo source: Jamila's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Matashiyar mawakiyar Hausa Hip Hop mazauniyar jihar Kano a halin yanzu, amma daga kasar saudiya wato "Jamila Jamcy" ta saki sabuwar wakar ta mai suna "Inta hayatee" hade da fefen bidiyan.


Mawakiyar wacce take karkashin kulawar fitaccen mawakin R & B Sonikman a matsayin manajan ta, ta saki wannan wakar ne a matsayin wakar ta na farko kwararre kuma bidiyan ta na farko. Jamcy ta na waka da harsuna uku wato harshen Hausa, Turanci da kuma Larabci.

Also Read: Rahama Sadau ta yi bangajiya ga mahalattan bikin dan uwan ta.


Wakar "inta hayatee" tini ta fara Jan ragama a wasu daga cikin shirye shirye na mawaka a gidajan radio da ke garin Kano, tin bayan da wakar ta doke wakokin mawaka irin su Hamisu Breaker, Umar M.Shareef, Dj Ab, Namenj, Mixter Ladagoma da kuma dai sauran manyan mawaka.


A cikin fefen bidiyan, an nuno fitaccen mawaki, makadi kuma ma'aikaci mai sarrafa sauti a Arewa24 wato "A-styl dbd" a matsayin saurayin ta a cikin bidiyan. Har yanzu dai ba mu samu sanarwar cewa mawakiyar ta na shirin sakin wani sabon aiki ba, amma akwai alamun nan kusa wani wakar ya fito daga wajan mawakiyar.

Top Stories

Burna Boy Featured in Justin Bieber's Upcoming Album 'Justice'

Top Trending New Naija Music Videos to Watch This Week

Latest Sinach Songs: Sinach Drops New Song 'Beautiful' Featuring Nathaniel Bassey

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Download Rema: Another Banger! ‘Bounce’, Rema Releases New Song (LYRICS)

Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

Leave your comment