Rahama Sadau ta yi bangajiya ga mahalattan bikin dan uwan ta.

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitacciyar jarumar Kannywood da kuma Nollywood Rahama Sadau ta yi jawabin godiya da ban gajiya da mahallatan bikin dan uwan ta Haruna Ibrahim Sadau (Abba Sadau) tare da Amaryar sa Zainab Musa Yarima. Bikin wanda ya gudana a jihar Kaduna cikin watan Janerun shekarar 2021.

Ya samu halattar manya manyan baki daga garurruwa daban daban musanman daga masana'antar finafinai ta Kannywood da jarumar ke cikin ta. A jawabin da Sadau ta wallafa a shafin ta na Instagram, ta ambaci sunayen manyan baki da su ka halacci bakin tare da mu su jinjina da godiya a bisa halatar bikin da su ka yi.

Ciki kuwa har da manyan mawakan irin su Umar M. Shareef da kuma Ado Isah Gwanja wanda duk su ka yi waka a wajan taron bikin. A mata jarumai kuwa, akwai irin su jaruma Fati washa wacce babbar aminiya ce ga Rahma sadau sai kuma irin su Ummul khair da mawakin ganbarar zamani wato Sojaboy da dai sauran manyan da su ka halacci bikin.

 

Also Read: Ali Jita ya yi kira ga jama'a da gwamnati akan yan Arewa a Oyo da Edo

Rahma sadau dai ta yi fice a manyan finafinai na Kannywood da Nollywood da dama, inda kuma a shekarun baya ta kara sanuwa bayan fitowar da ta yi a fefen bidiyan shahararren mawaki ClassiQ mai taken "I love you", wacce jarumar ta sha suka sosai a gun masoya da ma su kallon finafinan Kannywood bisa yadda ta yi rashin da'a a cikin fefen bidiyan ta hanyar rugume rugume da taba jikin juna da su ka yi tare da mawaki Classiq din.

Ko a kwanakin baya sai da jama'a da wasu jarumai a Kannywood su ka yi Allah wadai da jarumar bayan da ta wallafa wasu hotuna mai baiyana jikin ta a waje. Hotunan da ya jawo wani mutum da ba musulmi ba, ya taba mutuncin fiyayyen halitta manzon Allah tsira da aminci su tabbata agare shi. Duk da dai daga baya ta goge hotunan tare da bayar da hakuri ga masoya da abokan aikin ta, hakan bai hana wa su su cigaba da kalubalantar jarumar ba akan irin shigar da ta ke yawan yi.

Bikin dai ya gudana cikin nutsuwa da kwanciyar hankali kuma anyi shagulgula da dama ma su jan hankali da nishadantarwa irin su raye raye, yan rawa da wadan su kayattatun shirye shirye. Daga nan muma dai muna fatan za su zauna cikin zaman lafiya da zuciya daiyiba.

Also Read

Lilin baba na shirin zagayan gidajan radiyo a Arewa.

Ahmad shanawa's New Born Baby

Yakubu Muhammad New Series Release

News on Namenj and Hamisu Breaker new song

An yi wa maganar jarumi Momo mumunar fahimta a radiyo

An yi bikin zagayowar ranar haihuwar mawaki Umar M. Sharsef

Mawaka hudu (4) da ake sa ran za su yi tashe a sabuwar shekara 2021 a cikin Kannywwod

Mawaki Lilin baba ya saki sabuwar bidiyo

Leave your comment