Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

Photo source: Dan's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Fitaccen mawaki kuma ma'aikacin radio dan asalin jihar Katsina wato "Dan sa'a" ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa a jiya lahadi 28 ga watan 2, 2021 cikin farin ciki.


Mawakin wanda a yan kwanan nan ne ya fito a cikin wakar hadakar da Deezell ya gaiyaci mawaka da dama daga jihohin Arewacin Najeriya, ya wallafa wa su hotuna da ya yi su a cikin shiga irin ta sarauta a shafin sa na Instagram Facebook da kuma Twitter.


Darurruwan masoya ne su ka dinga yi wa mawakan fatan alheri tare da addu'oyin dacewa da kuma karin daukaka. Dan Sa'a wanda daya ne daga cikin manyan mawaka a jihar Katsina wanda ya ke waka da yare biyu wato harshen Hausa da turanci. Kuma ya yi waka a salon gambarar zamani wato Rapping da kuma salon R & B, ya bada gudunmawa matuka a tafiyar masana'antar Hausa Hip Hop ta jihar Katsina tin kafin fara aikin sa a gidan radiyo ta Ray power da ke garin Katsina, wanda tin kuma wannan lokacin ne Dan Sa'a ya ke sanya wakokin mawaka daban daban ta cikin shirin Top ten da ya ke yi a duk ranakun Asabar.


Dan Sa'a na shirin fitowa da kundin wakoki a sabuwar shekarar nan da mu ke ciki wanda kawo yanzu bai sanar da mai nene sunan sabuwar kundin na sa ba, amma lokaci kawai mu ke jira mu ga mai mawakin zai sanar akan kundin na sa wacce za ta fito nan ba da da jumawa ba.

Leave your comment