Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Photo source: Emir's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Fitaccen matashin mawakin Hausa Hip Hop wato Fresh Emir "Aku mai bakin magana" ya yi aikin wani bidiyo jiya lahadi a jihar Kano, wakar da mawakin ya yi akan yada jitajita da labaran bogi ya samu dauka tare da umarni daga Daracta Msk da tallafin Daracta Mus'ab Hausatop.


Mawakin tin bayan liyafar cin abinci da masoyan sa su ka hada mai a yan kwanakin nan, ya fara aikin bidiyan jiya da misalin karfe hudu na yanma bayan da a shekaran jiya mawakin ya halatti wata zagaye da kwamnatin Kano ta shirya dan kewaya wasu kananan hukumomi akan illar shayeshaye da hanyar magance ta.

Also Read: Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March


A kwanakin baya ma mawakin ya yi waka a gaban mataimakin gwamnan Kano Dr Nasiru Gawuna, a wani taron karramawa da aka shirya a cikin jamiyar B.U.K da ke garin na Kano.

Shima dai kamar sauran mawakan Hausa Hip Hop a shekarar nan ta 2021, ya shirya tsaf dan fara aikin fitar da wani kundin wakoki da ya ke yunkurin saki a shekarar nan da mu ke ciki. Aku mai bakin magana kamar yadda ake kiran shi, ya na da masoya da ke bin shi a shafin sa na Instagram mutun dubu dari da shiga, yayin da shi mawakin ke bin mutun dari uku da yan kai.

Latest News

Burna Boy Featured in Justin Bieber's Upcoming Album 'Justice'

Top Trending New Naija Music Videos to Watch This Week

Latest Sinach Songs: Sinach Drops New Song 'Beautiful' Featuring Nathaniel Bassey

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Download Rema: Another Banger! ‘Bounce’, Rema Releases New Song (LYRICS)

Hussaini Danko na shirin sakin sabuwar waka

Leave your comment