Yan Kannywood sun shirya wasan kwallon kafa a madadin dan uwa a masana'antar; Musty Dan ko

Photo source: Hamisu Breaker's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Jarumai a masana'antar Kannywood sun shirya buga wasan kwallon kafa yau talata 2 ga watan 3 na shekarar 2021 a filin motsa jiki da wasanni na zamani na dan kwallon kafa "Ahmad Musa", a madadin dan uwa abokin aiki a masana'antar Kannywood wato "Musty Dan ko" na daurin auran sa ta ya taso a cikin makon nan.

Also Read: Hamisu Breaker ya saki sabuwar bidiyo bayan bidiyan sa na Yadda kunne ya ji

Sanarwar ta fito ne daga shafin babban daracta Aminu S. Bono a Instagram, yau din nan. Ba wannan bane karo na farko ba, musanman idan biki ko daurin aure ko wani abu na cigaba idan ya taso wa daya daga cikin su. Kuma wannan karon ma hakan abun take, akan bikin "Musty Danko". Irin wannan abun ne ke saka dankon zumunci a tsakanin jaruman, domin har kullum kallon da masoya ke wa jarumai kenan " Tsinsiya madaurin ki daya". Anan dai sai dai mu ce Allah ya sa irin wannan zumuncin da alakar kusanci da kara da ake wa juna, zai daure a hakan, to masana'antar zai cigaba da habaka fiye da yadda take a halin yanzu.

Latest News

Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment