Hamisu Breaker ya saki sabuwar bidiyo bayan bidiyan sa na Yadda kunne ya ji

Photo source: Hamisu Breaker's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Mawaki fitacce mai tashe a masana'antar Kannywood a halin yanzu kuma daya daga cikin wadan da su ka sauya akalar waka a zamanance wato "Hamisu Breaker" ya saki fefen bidiyan wakar sa mai taken "Kanwata" a cikin satin nan da mu ke ciki. Wannan wakar waka ce da mawakin ya kwana biyu da fitar da ita kuma ta samu karbuwa sosai a wajan masoya, sai gashi babu shiri mawakin ya fitar da fefen bidiyan wakar.

Also Read: Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare
A kwanakin baya mawakin ya fitar da fefen bidiyan wakar "Yadda kunne ya ji" wanda su ka yi tare da jaruma "Mommy Gombe", kuma ta samu karbuwa sosai a wajan masoya, yayin da wa su kuma su ke ganin bidiyan bai yi kyan da su ke tsanmani ko sa rai ba.

Sai dai hakan bai rage yadda mawakin ke kara mamaye Arewacin kasan nan tere da zama daga cikin manyan mawakan da Arewa ke alfahari da su ba, inda hakan ya sa mawakin ya fitar da wannan sabon fefen bidiyan dan cigaba da rike kambun sa a duniyar manyan mawakan da masana'antar Kannywood ke alfahiri da tutiya da su.

Mawaki mai tasowa kuma dan asalin kasar Nijar haifefen Nigeria Ahmad Delta ne ya wallahi kadan daga cikin fefen bidiyan kamar yadda mawaka da jarumai da dama su ka yi kara wajan wallafa fefen bidiyan na sa a shafikan su na Instagram.

Latest News

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment