Mawakan Hausa Hip Hop sun dambatu a wani hotel

Photo source: Gwar Loaded

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Fitattun matasan mawakan Hausa Hip Hop "Madox tbb" dan jihar Kano da kuma Mr 442 dan garin Zaria da ke jihar Kaduna. sun yi danbe tare da fashefashe a tsakanin su cikin wani hotel a jihar Kaduna ranar lahadi 2 ga watan maris 2021. Fadan ya faru ne a lokacin da 442 ya danno cikin dakin da Madox ke ciki a wani babban hotel da ke Yakubu Avenue a jihar Kaduna.

Kamar yadda wasu fefen bidiyo biyu daga shafin Gwariloaded su ka nuna, inda a cikin bidiyon farko aka nuno 442 ya na tada jijiyar wuya inda shi kuma Madox ya taso daga inda ya ke a zaune ya farwa 442 din da kokowa. Sai fefe na biyu da ya nuna shi 442 din ya na ta masifa ana bashi hakuri dan ya koma dakin sa.

Also Read: Yan Kannywood sun shirya wasan kwallon kafa a madadin dan uwa a masana'antar; Musty Dan ko


Tin a ranar asabar da ta gabata ne, aka ga mawakan Hausa Hip Hop da dama daga jihohi daban daban a jihar Kaduna gurin wani wakar hadaka da mawaki Deezell mazaunin kasar Amurika ya hada, inda aka ga irin su Dj Ab, Dabo Daprof, Lil prince, L.x Vee, Larabee, Mai dawa, 442, Liya, Cdeeq, Ovister, triple D, Boyskiddo, X. Boy da shi kansa Deezell din. inda shi 442 na daga cikin mawakan da aka gaiyata cikin wannan wakar hadakan.

Amma abun mamaki shi ne yadda mawaki Madox tbb dan asalin jihar Kano ya baro garin Zaria inda ya ke makaranta a jamiyar A.B.U, ya taho Kaduna duk kuwa da babu shi a cikin mawakan da ke cikin wanchan aikin, kuma ya sauka a hotel din da aka sauke mawakan cikin har da abokin fadan na sa 442. Jin cewa Madox na cikin wannan hotel ne, 442 ya fara bi daki daki ya na neman sa, kuma ganin shi ke da wuya su ka kaure da fada.

Other News: Hamisu Breaker ya saki sabuwar bidiyo bayan bidiyan sa na Yadda kunne ya ji

Har yanzu mawakan biyu sun ki baiyana musabbabin rigimar ta su, duk kuwa da bibiyar su da madubi Naija ta yi hakan ya citira, amma manajan Madox YK Designer dan nan garin Kano, ya baiyana bakin cikin sa akan wannan abu da ya faru tsakanin mawakan biyu wanda abokai ne.

Latest News

Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment