Nazifi Asnanic ya fitar da sabuwar wakar sa

Photo source: Nazifi Asnanic's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Fitaccen mawaki, mai shirya finafinai da kuma bada umarni, kuma daya daga cikin mawakan siyasa "Nazifi Asnanic" ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Ban ci amana ba" a man'ajar Audiomack. Sabuwar wakar wadda matashin makadi kuma jarumi Amude Booth ya yi aikin wakar ta fita ne a kwanakin baya a wasu man'ajojin na daban.

Amma tin a wannan lokacin wakar ba ta fito ba a man'ajar Audiomack ba sai a wannan makon na farko a cikin watar maris ta 2021. Inda mawakin ya wallafa sanarwar fitar wakar a shafin sa na Instagram. Nazifi Asnanic wanda ya shura a masana'antar Kannywood shekara da shekaru, na daga cikin mawakan da ake wa kallon sun juma su na sharafi kuma har yanzu ta na yi da su.

Also Read: Mawakan Hausa Hip Hop sun dambatu a wani hotel

Inda bayan waka da a ka fi sanin mawakin da ita, ya kara fadada basirar sa a fanin shiryawa, daukan nauyi da kuma ba da umarni a finafinai daban daban na kwanfanin sa da ma na wasu mutanan. "Labarina", sanan nan fim ne a halin yanzu wanda ake haskawa a tashar Arewa24, kuma Nazifi Asnanic na daya daga cikin wadan da su ke daukan nauyin wannan fim din.

Haka zalika akwai wasu aiyukan kungiyoyi manya ma su zaman kan su na (NGO), da mawakin ke wa aiyuka daban daban.

A sannin wakokin siyasa, Nazifi Asnanic na daga mawakan da wakar su ta yi tasiri a zaban tsohon gwamna kuma tsohon sanata "Dr Rabiu Musa Kwankwaso" wajan cin zaben gwanma a karo na biyu a jihar Kano.

Wannan sabuwar wakar ta Nazifi Asnanic mai taken "Ban ci amana ba" na dauke ne da salon zamani irin na Afro pop da kuma salon rauji duk a hade cikin kidan, kuma wakar na dauke da sako mai ma'ana da shiga jikin duk wani mai sauraro.

Latest News

Mawakan Hausa Hip Hop sun dambatu a wani hotel

 

Yan Kannywood sun shirya wasan kwallon kafa a madadin dan uwa a masana'antar; Musty Dan ko

Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

 

Leave your comment