Makadin jita da hannaye biyu David Swauzo ya fitar da sabuwar waka bayan dawowar sa Najeriya.
9 March 2021
Photo source: David Swauzo 's Instagram handle)
By Omar Ayuba Isah
Join Mdundo's Telegram Channel
Matashin mawakin Hausa Hip Hop, makadi, kuma makadin Jita da hannun dama da na hagu wanda a turance ake ce da su " Ambidextrous Guitarist " David Swauzo ya fitar da sabuwar wakar sa mai taken "Daga Allah ne" a shafin nan na sauraron wakokin na Haske247 da ke nan kasar Najeriya.
David Swauzo tin bayan dawowar sa Najeriya daga kasar Sudan, Inda mawakin ya yi kusan shekara guda ya na zagayan jiha bayan jiha tare da ragowar makada daga kasashe daban daban dan yin wasanni a wuraren shakatawa da ke kasar Sudan din ne, ya ke ta shiryeshiryen sakin wakoki da ya yi a kasar Sudan tare da wa su mawakan da su ka hadu a chan kasar.
Daga dukkan alamu dai mawakin ya gama shiri, domin a cikin satin nan da mu ka baro ne mawakin ya wallafa hoton wannan waka da kuma sanarwar fitowar ta a wannan shafi ta Haske247. David Swauzo wanda dan jihar Kano ne ya fara waka ne tin a yarinta lokacin da ake na choci da shi, wanda kuma yanzu ya ke cigaba da bada gudunmawa a wakokin chocin da kuma a salon reggae, afro beats da kuma hip hop.
Also Read: Bayan danben kece raini, Madox da 442 sun yi sulhu a tsakanin su har sun fitar da sabuwar waka tare.
Babban baiwan David Swauzo bayan waka da aka san shi da ita, shi ne baiwar sa ta kada jita da hannun dama da kuma hannun hagu kuma ko wanne ya kware a kai. A makon nan da ya wuce ma mawakin ya fito a wani fefen bidiyo na babban mawaki Billy-O mai taken "Ina son ki", inda aka nuno shi ya na kada jita a cikin bidiyan.
Wa su daga cikin wakokin da David Swauzo ya yi a baya sun hadar da " Nagode ", " "Slogan", wacce ya yi ta a matsayin sadaukarwa ga manyan mawakan Hausa Hip Hop da su ke da inkiya. Sai sabuwar wakar " Daga Allah ne" da dai sauran su.
Latest News
Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.
Makadin jita da hannaye biyu David Swauzo ya fitar da sabuwar waka bayan dawowar sa Najeriya.
Isah Ayagi ya fara tallata sabon kundin sa.
Abun da ya sa wakokin Hausa ba sa sanu a duniya kamar na ragowan wakokin kudu ba
Leave your comment