Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.

Photo source: ALi Nuhu's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Fittaccen jigo kuma babban Jarimi Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon Fim mai suna "Zabin Raina" wanda a halin yanzu a ke cigaba da daukan aikin a jihar Jigawa. Yaya Muhammad shi ne mai shirya wannan fim din, rdbawa ya ba da umarni, labari da tsarawa kuwa Mujahid s. Koguna.

Mawakan da su ka yi waka a cikin wannan fim din sun hadar da Umar M. Shareef, Ahmad Delta, Musty Knaisa, Yaya Muhammad da kuma Aliyu S. Marafa. Jarumai kuwa da ke cikin wannan fim sun hada da Ali Nuhu, TY Shaban, Babanle Ayatu, Umar Gombe, Ainau Ade, Humairatuh, Ali Rabiu Ali Daddy, Miemie, Nana Sadeeq, Salisu Fulani, Stephanie Dadinkowa, Ahmed Bello, Aseeyah Aliyu, Ikilima Yusuf, Meenat, Mustapha Badaru da kuma Fatima Hamza. Wadan nan su ne jaruman da su ka taka rawar ganin a cikin wannan fim mai suna "Zabin Raina".

Sanarwar fara daukan aikin wannan fim ya fito ne daga shafin Daracta Aminu S.Bono na Instagram.

Leave your comment