Feezy ya saki bidiyo daya a cikin kundin sa ta Kingdom.

(photo credit: from FeezyM-kay

's official Instagram page)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Kaduna "Feezy" kuma kani ga babban mawakin Hausa Hip Hop "Dj Ab", ya fitar da sabuwar fefen bidiyan wakar " Me ya rage" wacce ita ce waka ta hudu kuma ta karshe a cikin kundin wakokin da ya saki mai taken "Kingdom" a wannan watan da ta kare ta Febureru.

A daran jiya laraba ne mawakin ya fitar da wannan fefen ta shafin sa na Instagram, inda bidiyan aka yi shi cikin daki mai takaitaccen haske kuma aka nuno mawakin akan gado kwance yana raira wakar.

Feezy wanda makadi ne mawaki ne kuma mai editing tare da daukan bidiyo, ya kasance daya daga cikin mawakan Arewa da ke da tarin basira kuma jigo a tafiyar kunyiyar nan ta mawaka a garin Kaduna mai suna Y.N.S wato "Yaran North Side". Kawo yanzu ba a san ko mawakin zai yi wa duk wakokin na sa bidiyo ba, amma alamu dai sun nuna a wannan shekarar ta 2021, Feezy ya shirya tsaf dan fitar da wakoki da bidiyo daban daban wasu kuwa a ciki har da wanda ya ke wa wasu mawakan aiki akai.

Latest News

 

Mawakan Hausa Hip Hop sun dambatu a wani hotel

Yan Kannywood sun shirya wasan kwallon kafa a madadin dan uwa a masana'antar; Musty Dan ko

Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

 Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment