Namenj ya fitar da sabuwar wakar sa tare da Hamisu Breaker

Photo source: Namenj's Instagram handle)

By Omar Ayuba Isah

Join Mdundo's Telegram Channel

Mawakin zamani mai salon wakokin Afro beat, kuma sananne a fannin juya wakokin da na mawakan Arewa izuwa daidai da zamani wato Namenj, ya fitar da sabuwar wakar sa mai taken "Dama" hade da bidiyan ta a makon nan da ta wuce. Ya kuma yi wakar ne tare da fitaccen mawaki dan yayi mai salon wakokin Hausa Nanaye wato Hamisu Breaker a karkashin kwamfanin nan na Mr Eazy wato "Empower Africa".


Namenj ya fitar da wannan wakar ne watanni da kawo ziyarar musanman jihar Kano, inda anan ne Hamisu Breaker ya ke zaune. Kuma ana ganin kamar anan ne ma su ka hadu har aka yi wannan wakar tare. Mawaki Namenj tin bayan sanuwar sa ga mabiyan wakokin Hausa a fadin duniya, ta cikin wakar shahararren mawaki Umar M. Shareef da ya juya ta izuwa salon Afro beat.

Also Read: Top 5 Latest Naija Songs:Final Say By Banky W, Bounce By Rema and More


Ko a kwanakin baya, Namenj ya fitar da wa su wakoki manya da ya yi wa video irin su " Fatana" da "Rayuwata". Sai wakar Dj Ab ta " Rai Na " da shi da Dabo Daprof su ke fito a cikin wakar a watan Nuwamba ta 2020. Wakar "Dama" ta Namenj din sabuwar waka ce da ke baiyana burin masoyi ga abar kaunar sa ta cewa Dama a ce ita ya fara sani a rayuwa, da ya juma da auren ta tintini.

Kuma wani abun burgewa a cikin bidiyan wakar shi ne yadda Namenj da Hamisu Breaker a ka nuno ko wannen su a cikin bidiyan sanye da kayan ma su saida abinci ko abin sha a gidan abinci wato "Restaurant ", kuma ahakan su ke baiyanawa abun kaunar su irin yadda su ke kaunar su. Tini dai wannan wakar ta fito a shafin YouTube na Empower Africa da sauran shafukan zamani da kuma man'hajojin sauke waka iri daban daban a duniya.

 

Latest News

Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.

 

Isah Ayagi ya fara tallata sabon kundin sa.

Abun da ya sa wakokin Hausa ba sa sanu a duniya kamar na ragowan wakokin kudu ba

Download Hausa Music:Top 5 Artists; Umar M. Shariff, Nura M. Inuwa, Isah Ayagi, Hamisu Breaker, Adamu Hassan Nagudu… (FREE Download)

Feezy ya saki bidiyo daya a cikin kundin sa ta Kingdom.

Leave your comment