Mawaki Umar MB ya fitar da sabuwar kundin waka

Picture source: Umar MB's official Instagram account

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Matashin mawaki dan asalin jihar Kaduna, kuma marubuci sannan mai editing video Umar M.B ya fitar da sabuwar kundin wakokin sa mai taken "Rai" a cikin wannan watar ta Maris da mu ke ciki ta shekarar 2021.

Wannan kundin mai dauke da wakoki har kwaya shida (6), mabanbantan salo da labari ya zo da wani sabon yanayin da ba haka aka saba ganin kundin wakokin Hausa na salon Nanaye ke fitowa.

Musanman idan aka yi la'akari da karancin wakokin da ke cikin wannan kundin ta "Rai" da Umar M.B ya fitar. Domin kundin wakokin Hausa na salon Nanaye kan dauki yawan wakoki da ya kai goma sha tagwas zuwa wakoki ashirin ma. Wa su kuma har kasa da hakan ma su na iya sakin wakoki a cikin kundi.

            Feezy zai saki ainahin bidiyan wakar Mai ya rage
Sunayen wakokin da ke cikin wannan kundin ta "Rai", sun hadar da wakoki irin su:
1- Aminta Dani

2- Rai

3- Rana

4- Ina son ki

5- Yafe ni

6- Wasika


Kuma tin fitowar wannan kundin ta Umar M.B, masoya da dama su ke kara baiyana gamsuwar su da irin salon wakokin da mawakin ya yi hade da girman aikin da aka yi wa wannan kundin.

Yanzu haka ana cigaba da yin challenge akan wa su daga cikin wakokin da ke cikin kundin dan kara tallata mawakin da ita kanta kundin.


Wadan nan wakoki za su kasance akan shafin mu na Mdundo nan ba da jumawa idan Allah ya nufa.

Masoyan Hamisu Breaker sun kai mutun miliyan daya a Instagram

Ana aikin wani sabon fim mai dogon zango irin sa na farko a Kannywood

Deezell ya baiyana sunayen mawakan da yake shirin dagawa a cikin sabuwar aikin da zai fitar.

Mawaki Lilin Baba zai fitar da sabuwar fim

Masana'antar Hausa Hip Hop ta sake babban rashi na wani mawakin

AleeGee ya taya jaruma Gabon murnar ranar mata ta duniya.

Leave your comment

Top stories

More News