Deezell ya baiyana sunayen mawakan da yake shirin dagawa a cikin sabuwar aikin da zai fitar.

 

Photo source: Nigeria Deezell

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Mawakin Hausa Hip Hop Deezell mazaunin kasar Amurika kuma dan asalin jihar Kano, Ibrahim Ahmad Rufa'i wanda aka fi sani da Deezell ya shirya fitowa tare da daga darajar wasu mawakan Hausa Hip Hop mutun shida ta cikin sabuwar wakar da zai fitar.


Mawakin ya sheda wa masoyan sa haka ne a shafin sa na Instagram a cikin wata hira da mawakin yayi da wani shafin wallafa labarai na nishadi a jiya laraba.


Deezell wanda tin a farkon shekaran nan ta 2021 ne ya fitar da wakar hadaka ta mawaka goma sha shida (16) mai taken "Duk abun da zai fara ya faru" wacce ta karade kofafan sada zumunci daban daban duba da jerin fasihen mawaka da ya gaiyato a cikin wakar.

Sai gashi a yan kwanakin nan an gano mawakin tare da wasu mawakan a jihar Kaduna inda su ke aikin wani sabon wakar su bakwai.

Deezell ya baiyana cewa dalilin sa na wannan wakar dan ya daga mawakan ne su shida da irin damar da ya ke da ita. Wanda dalilin wannan aikin ne mawakin ya dauko kamarar sa tin daga kasar Amurika izuwa Nigeria dan a samu irin hoton da ake da bukata.


Mawakan sun hadar da Triple daga kano, Cdeeq daga kano wanda manajan Deezell din ne kuma mawaki, Boyskiddo daga sakwato, Mr 442 daga garin Zaria, Lxvee daga Kaduna, Lil Prince daga Kaduna sai kuma shi mai gayya mai aiki Deezell.


Kuma Feezy ne ya dauki wannan aikin bidiyan sannan ake sa ran fitar aikin anan kusa kusa.

 

Leave your comment

Top stories