Masana'antar Hausa Hip Hop ta sake babban rashi na wani mawakin

Photo source: Hafsa News

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Kwanaki ashirin da masana'antar Hausa Hip Hop ta tashi da alhinin labarin rasuwar matashiyar mawakiyar nan yar jihar Kano mai suna "Mamo Oosha" masana'antar ta sake wayan gari da mumunan labarin mutuwar Matashin mawaki makadi kuma mai halittar zabi "Sani Abbas", wanda duniya ta sani da inkiyar "Aybeewon".

Mawakin wanda ya mutu sakamakon kashe shi da aka yi ta hanyar chaka mai wuka a gurare da dama a jikin sa cikin dare. A daf da gidan da mawakin ke zaune ciki a garin Abuja dake Najeriya.

Inda mawakin ya dinga zubar da jini har ya mutu kafin a kawo mai wani agajin gaggawa. Aybeewon wanda ya yi makaranta a jami'ar A.B.U da ke Zaria a jihar Kaduna, wanda kuma ke zaune a babban birnin taraiya Abuja, inda kwana daya da dawo wa Abujan ne mawakin ya gamu da ajalin sa.

Mutuwar sa ta zo ne a daidai lokacin da mawakin ke jan ragama a cikin gasar da wani fitaccen mawakin kudu da aka fi sani da Shmurda Bella ya saka a kwanannan, inda mawakin ke da kimanin wadan da su ka saurare shi mutane dubu 57 da dari 5, wanda hakan babban nasara ce ga mawakin. Sai dai ashe ba rai ake yi wa ba kuma tini aka yi jana'izar sa kamar yadda addinin musulinci ya tanada.

Muna taya iyalan wannan mawakin jaje da kuma alhinin wannan rashi, fatan Allah ya jikan shi da rahma amin.

Leave your comment

Top stories