Feezy zai saki ainahin bidiyan wakar Mai ya rage

Photo source: Youtube Feezy

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Kaduna "Feezy" kuma kani ga babban mawakin Hausa Hip Hop "Dj Ab", zai fitar da ainahin fefen bidiyan wakar " Me ya rage" wacce ita ce waka ta hudu kuma ta karshe a cikin kundin wakokin da ya saki mai taken "Kingdom" a wannan watan da ta kare ta Febureru. Ita kuma fefen bidiyan sai fito 14 ga wannan wakar ta Maris.

Bayan yan kwanaki da mawakin ya fitar da wani dan guntun fefen ta shafin sa na Instagram, inda bidiyan aka yi shi cikin daki mai takaitaccen haske kuma aka nuno mawakin akan gado kwance yana raira wakar.

Feezy wanda makadi ne mawaki ne kuma mai editing tare da daukan bidiyo, ya kasance daya daga cikin mawakan Arewa da ke da tarin basira kuma jigo a tafiyar kunyiyar nan ta mawaka a garin Kaduna mai suna Y.N.S wato "Yaran North Side". Kawo yanzu ba a san ko mawakin zai yi wa duk wakokin na sa bidiyo ba, amma alamu dai sun nuna a wannan shekarar ta 2021, Feezy ya shirya tsaf dan fitar da wakoki da bidiyo daban daban wasu kuwa a ciki har da wanda ya ke wa wasu mawakan aiki akai.

Deezell ya baiyana sunayen mawakan da yake shirin dagawa a cikin sabuwar aikin da zai fitar.

Ana aikin wani sabon fim mai dogon zango irin sa na farko a Kannywood

Mawaki Lilin Baba zai fitar da sabuwar fim

Umar M. Shareef ya samu karuwa a satin nan

Leave your comment

Top stories