Mawaki Lilin Baba zai fitar da sabuwar fim

Photo source: Hausa highlights

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mawakin Hausa Hip Hop kuma dan kasuwa dan asalin jihar Kaduna "Lilin Baba" ya shirya fitar da sabuwar fim din sa mai suna "Wuff" a karkashin kwamfanin sa ta "Northeast records".

Wannan sabuwar fim da Lilin Baba ya fara tallatawa a shafukan sada zumunci na zamani, ya na dauke da hotunan wasu manyan jarumai da su ka taka rawar gani a ciki, irin su babban jarumi Ali Nuhu, Abdul M. Shareef, Hajiya Fati, Azima gidan badamasi da shi kan sa Lilin Baban wanda zai fito a karo na farko cikin fim tare da wa su jarumai biyu suma sababbi kamar Xee Natiti da Najmar Husaini.

A lokacin da ake cigaba da sauraron sabon kundin mawakin mai suna " Sound from the North" a gidajan radio daban daban da sauran man'hajojin sauke wakoki na zamani, sai ga mawakin Hausa Hip Hop din ya fito da wannan sanarwar da ta baiwa masoyan sa farin cikin ji.

Kawo yanzu dai mawaki Lilin Baba bai baiyana ranar fitowar wannan sabon fim ba na kwamfanin sa, amma ya baiyana cewa wannan matakin farko kenan a shiryeshiryen sa na tallata wannan sabon fim na sa mai taken "Wuff" wanda hakan sara ce sananniya da kwana kwanan nan ne ake yawan amfani da shi.

Leave your comment

Top stories