Umar M. Shareef ya samu karuwa a satin nan

Photo source: Nigeria Hausa Updates

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Babban mawakin Hausa na salon Nanaye kuma matashin jarumi a finafinan Kannywood Umar M. Shareef dan asalin jihar Kaduna ya samu karuwa na Ya' mace a karshen makon nan da mu ka yi bankwana da shi na watan Maris 2021. Umar M. Shareef wanda ya yi wannan sanarwar a shafin sa na Instagram wanda sama da mutane miliyan daya da dubu dari biyu ke bin sa a kai, inda ya sanar da masoyan sa wannan labarin karuwar tare da baiyana cewa lafiyar mahaifiyar lau, ita kuma Yar ta sa da ya sanyawa suna "AMEENAH", ya ke rokan mata lafiya da kuma albarka.


Umar M. Shareef wanda kwanan nan ya saki sabuwar wakar sa mai taken" Lagwada", wanda Selebobo babban mawaki kuma makadi a Najeriya ya mai aikin wannan wakar, ya kuma sanar cewa fefen bidiyo na wannan waka zai fito nan ba da jumawa ba. Mawaki ne wanda masana'antar Kannywood da ta waka irin salon Nanaye ke alfahari da yadda mawakin ke cigaba da daga darajar yaran Hausa da al'adun ta a idon duniya.


Mawaki Umar M. Shareef na daga cikin mawakan Hausa da su ke da aure amma ba kowa ya san da hakan ba duba da shekarun da mawakin ya yi da aure kafin ma ya kai wannan matsayin a daukaka. Muna fatan alheri ga mawaki Umar M. Shareef da wannan karuwar, Allah ya raya Ameenah Amin summa Amin.

Leave your comment