Masoyan Hamisu Breaker sun kai mutun miliyan daya a Instagram

Photo source: Nigeria Hausa Updates

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Babban mawakin Hausa na salon Nanaye kuma mawakin da ake yayi a halin yanzu wato "Hamisu Breaker" ya yi murnan samun yawan masoya a shafin Instagram har mutun miliyan daya.


Mawakin ya wallafa hoton na musanman ne dauke da rubutun farin ciki tare da godiya ga masoyan sa a bisa wannan matakin da mawakin ya kai. Hamisu Breaker yanzu na daga cikin mawakan da su ke da mabiya a shafin Instagram da adadin su ya wuce miliyan, kuma a cikin dan kankanin lokaci mawakin ya kai wannan matakin.

Feezy zai saki ainahin bidiyan wakar Mai ya rage

Hamisu Breaker wanda wakokin sa su ke cigaba da karbuwa a gurin masoyan wakokin Hausa na salon Nanaye a fadin duniya, matashi ne a shekaru kuma wanda a kwanan nan ne su ka yi hira da jaridar BBC Hausa, inda ya baiyana cewa ba shi da aure amma ya na neman abokiyar zama ta gari. Sannan kuma mawakin ya musalta zargin sa da ake yi da shaye shaye, inda ya ce halittar sa ce hakan amma ba dan wai ya na yi bane.

Muna fatan mawaka daga arewa za su cigaba da samun irin wannan mabiya ma su yawa dan samun kwagilan talla daga manyan kwanfanunnuka a duniya.

Dj Ab zai bude sabuwar kwamfanin hadahada.

Umar M. Shareef ya samu karuwa a satin nan

Deezell ya baiyana sunayen mawakan da yake shirin dagawa a cikin sabuwar aikin da zai fitar.

Mawaki Lilin Baba zai fitar da sabuwar fim

Leave your comment

Top stories