AleeGee ya taya jaruma Gabon murnar ranar mata ta duniya.

Photo source: AleeGee 'a's Instagram highlights)

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Fitaccen mawakin Hausa Hip Hop kuma makadin zamani, AleeGee wanda ya ke Wa kan sa lakabi da "Ali zaki" a jiya ya taya shahararriyar jarumar Kannywood Hadiza Gabon murnar ranar mata ta Duniya da a ka yi bikin jiya 8 ga watan Maris 2021.

Mawakin Hausa Hip Hop din ya wallafa hoton sa ne tare da fitacciyar jarumar a shafin sa na Instagram tare da rubutun taya murna ga jarumar a bisa wannan ranar ta mata ta Duniya da ake bikin sa jiya.


Wani abun burgewar shine yadda jaruma Hadiza Gabon ta mayarwa mawaki AleeGee martani a karkashin hoton na su da ya wallafa, inda ta ke masa godiya da yabawa bisa karamcin sa gare ta. Wanda kuma masoyan sa da dama su ka baiyana farin cikin su ga wannan martani da Hadiza Gabon ta yi wa AleeGee.

Also Read: Mai shadda na shirin fara haska sabuwar fim din kwamfanin sa a wannan wakar ta Maris
AleeGee wanda daya ne daga manyan matasan mawakan Hausa Hip Hop daga garin Kano dan asalin jihar Katsina, ya na cigaba da tallata rubutaccen fefen bidiyan wakar sa mai taken "Ko dan Mata" wanda ta karbu sosai a cikin wakokin sa.

Alakar AleeGee da jaruma Hadiza Gabon abu ne dadadde kuma ana ganin mawakin ya kasance daya ne daga manyan masoyan ta inda kullum shafukan sa ke dauke da hotuna ko yabo ko magana akan jarumar daga babban mawakin gambarar zamanin.

Dan samun labarai da muhimman abubuwan sani game da wakokin Hausa, ku cigaba da bibiyar mu a Mdundo

Dan Sa'a ya fitar da sabuwar waka daga cikin kundin da zai saki.

Leave your comment

Top stories