Mai shadda na shirin fara haska sabuwar fim din kwamfanin sa a wannan wakar ta Maris

Photo source: Shadda's Instagram highlights)

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Shahararren mai daukan nauyin finafinan masana'antar Kannywood Abubakar Bashir, wanda aka fi sani da (Mai shadda) ya fara shirin fitowa da wani sabon fim din sa mai suna "Tsakanin mu" a cikin watan nan da mu ke ciki ta maris a shekarar 2021.


Wannan fim da za'a fara haska shi a gidan kallo (Film House) da ke Ado Bayero Mall a ranar 26 ga watan Maris, ya hada manya manyan jarumai a cikin wannan fim mazan su da mata, kuma ko daga sunan wannan fim, za ka san akwai labari mai daukan hankali a cikin wannan sabon fim na Mai Shadda, wanda zai fitar a karkashin kwamfanin sa ta "Maishadda Global Resources Ltd.


Wasu manyan jarumai da ke cikin wannan fim sun hada da irin su babban jarumi Ali Nuhu, Yakubu Muhammad, Baballe Hayatu, Abba Elmustapha, Maryam Booth, Maryam Yahaya, Umar M.Shareef, Ainau Ade, Husaini Nura, Anas Magu, Asmau Sani, Yusuf Saseen, A. Hajjaju, Munat kwana chasa'in, Kabir Saddiq da kuma Kamal I. Hikima. Sai kuma sauran jarumai kanana da su ma su ka taka rawa a cikin wannan fim mai taken" Tsakanin mu".

Also Read: Dan Sa'a ya fitar da sabuwar waka daga cikin kundin da zai saki.


Mawakan da su ka rera wakokin da aka yi anfani da su a cikin wannan fim din su ne Umar M. Shareef da kuma Abdul D One. Jarumi Ali Nuhu ne ya bada umarnin wannan fim, Sheik Isa Alolo mataimakin mai bada umarni, Nelcon 24 ya nadi wannan fim din a camera, Media suite su ka yi editing, da sauran mutanan da su ka yi aiki mabanbanta kafin kammaliwar wannan fim din.

Tini mabiya finafinan masana'antar Kannywood su ka fara tafka mahawara akan wannan sabon fim din da zai fito a sati uku ma su zuwa.

Latest News

New Naija Music Videos To Watch This Week: Featuring Fireboy DML, Niniola

Simi, Tiwa Savage, Teni, Wande Coal Featured in Mr P's 'Prodigal' Album (FULL TRACKLIST)

Makadin jita da hannaye biyu David Swauzo ya fitar da sabuwar waka bayan dawowar sa Najeriya.

Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.

Latest Songs Naija: 7 Top Trending

Leave your comment