Dan Sa'a ya fitar da sabuwar waka daga cikin kundin da zai saki.

Photo source: Dan Sa'a's Instagram highlights)

By Omar Ayuba Isah

Get Free Music Updates and Mixes on Telegram

Mawakin Hausa Hip Hop dan asalin jihar Katsina da ke aiki a radio Dan Sa'a ya saki sabuwar wakar sa mai taken "Lahiya lau". A cikin satin nan da mu ke ci na watan maris 2021wannan wakar ta fito a matsayin daya daga cikin jerin wakokin da mawakin ke shirin fitarwa a cikin sabon kundin sa.

Wannan kundi da mawakin bai baiyana wakoki na wa ke ciki ba ya kunshi mawaka manya irin su Deezell mazaunin kasar Amurika, Chizo Germany mazaunin kasar Jamus, Dabo Daprof sanannan mawaki dan asalin jihar Kano da dai sauran su a cikin wannan kundin.

Also Read: Bayan danben kece raini, Madox da 442 sun yi sulhu a tsakanin su har sun fitar da sabuwar waka tare.


Dan Sa'a wanda a cikin wannan sabuwar shekarar ya fito a cikin wakar hadakan nan ta " Duk abun da zai fara ya faru", wanda mawaki Deezell ya hada tare da gaiyatar mawaka mutun goma sha shida (16), ciki har da su Dj Ab, Feezy, Chizo Germany da sauran su.

"Lahiya lau" waka ce dauke da salon barkwanci, nishadi da kuma rawa duk a guri daya. Sannan waka ce da ke jan hankali ga wasu abubuwan da mutane ke mu'amala da su na yau da kullum a tsakanin su.

Dan Sa'a wanda ya na waka a salo biyu wanda da su ya sanu a masana'antar Hausa Hip Hop, wato Rapping (gambarar zamani) da kuma Singing (rerarriyar waka a sanyin murya). Kuma ya na daya daga cikin manyan mawaka da jihar Katsina ke alfahari da su a Hausa Hip Hop kuma ya bada gudunmawa mai tarin yawa ga mawaka ma su tasowa a masana'antar tin fara aikin sa a gidan radio ta Ray power dake jihar Katsina.


Dan samun labarai da muhimman abubuwan sani, ku cigaba da kasancewa da Mdundo a koda yaushe.

Latest News

New Naija Music Videos To Watch This Week: Featuring Fireboy DML, Niniola

Simi, Tiwa Savage, Teni, Wande Coal Featured in Mr P's 'Prodigal' Album (FULL TRACKLIST)

Makadin jita da hannaye biyu David Swauzo ya fitar da sabuwar waka bayan dawowar sa Najeriya.

Ali Nuhu ya fito a cikin wani sabon fim da ake dauka a halin yanzu.

Latest Songs Naija: 7 Top Trending

Leave your comment