Sauke wakokin Hausa daga fitatttun mawaka 5: Umar M. Shareef, Nura M. Inuwa, Isah Ayagi, Hamisu Breaker da Hassan Nagudu...(Duk a kyauta ta shafin Mdundo)

[Image Source: www.psdtolive.com]

Join Us on Telegram

Yanzu kai tsaye za su iya sauke tare da sauraron wakokin Hausa a kyauta ta shafin mu.

Har yanzu duniya ba ta kai ga sani tare da dandana tarin dadi da ma'ana hade da ilimi daga wakokin Hausa. Sanannun mawakan Hausa ma su salon Nanaye gwanaye ne kuma duk inda ka ke a duniya za ka iya samu tare da sauraron wakokin su kai tsaye dan nishadantuwa da dadadan salon wakokin mawakan Hausa da ke Afirika.

Also Read: Umar M. Shareef ya fitar da sabuwar waka a karshen watan nan da ta kare

Wakokin Hausa sun bada gudunmawa mara musaltuwa, a salon wakoki mabanbanta a nahiyar Afirika a halin yanzu. Mawakan Afirika da dama sun yi aron salo da kalamai daban daban daga wakokin Hausa, wanda hakan ya sa su ka samu karbuwa da kuma sanuwa a duniya cikin su har da shahararren salon wakan nan da aka fi sani da Afro Beatz., Afro Pop da kuma Afro soul da ma sauran su.

Yau za mu yi duba ga mawaka 5 fitattu daga Arewacin Najeriya kuma mawaka ma su salon wakokin Nanaye, wadan da duk za a iya samun wakokin a shafin mu na Mdundo.

1. Umar M Shariff

...gogagge, fitacce, kwararre kuma tauraro a mawaka, dan garin Kaduna. Sabon aikin sa babba da ya fitar yan kwanakin bayabayan nan shi ne kundin sa na "Zuciya" wanda ya fito a shekarar 2020.

2. Nura M Inuwa

Babban mawakin Hausa na Afrika kuma mai sarautar inkiya na "jakadar baitukan Hausa". Nura har ilahi yau, jakada ne ga jamiyar kudi ta "MA'AUN", wato Jamiyar Maryam Abacha ta kasar Nijar da ke garin Maradi. Ita ce jamiya ta turanci ta farko a kasar Nijar kuma ta farko mai koyarwa da harsuna biyu a yankin Afrika ta yanma da ma gabashin Afrikar.

 3. Isah Ayagi

Fitaccen mawakin zamani wanda a halin yanzu ya ke aiki akan sabuwar kundin sa mai taken "Hasken Ruhi"

4. Hamisu Breaker

Mawaki mai sharafi kuma tauraro a masana'antar wakokin Hausa na salon Nanaye, wanda tin bayan fitowar wakar "Jaruma" daukakar sa ta kara daukan sabon salo. Mawakin wanda ya samu sunan sa ta Breaker a lokacin da ya ke koyan rawa, kafin daga bisani ya koma waka gadangadan.

5. Adamu Hassan Nagudu

Mawakin Hausa dan kasan Najeriya wanda ya yi fishe a wakar sa ta "Jaye Mamma". Adamu ya cigaba da fitar da zafafan wakoki irin su " Buri na" da kuma kundin nan ta "Rike Gwanin ka".

Mdundo Hausa Mixes 

Wakokin Gamaiya ta Dj daga Mdumdo a kyauta dan nishadantuwar ka, tare da sanin labarin sababbin wakoki idan su fito, da kuma bayane akan mawakan ku da wakokin su ke kan man'hajan mu ta Mdundo.

 

Latest News

Mawaki Dan Sa'a ya yi bikin zagayowar ranar haihuwar sa jiya

Fresh Emir ya fara sabon aikin bidiyo

Mixterbash na shirin bude gidan radio a watan March

Billy-O Ya Saki Sabon Bidiyo Na Barko Bayan shekaru: "I Love You"

Shahararen mawakin R & B Sonikman mazaunin jihar Kano ya saki sabuwar wakar "Mama Yeah"

Leave your comment