Nura M. Inuwa zai saki sabuwar waka

By Omar Ayuba Isah

Tura wa aboki ta WhatsApp

Fitaccen mawakin Kannywood, daya daga cikin manyan mawakan zamani biyu da su ka fi ko wani mawaki a mawakan wakokin rauji wato yan "Nanaye" jumawa su na tashe kuma mai shirya finafinai a masana'antar ta Kannywood wato Nura M. Inuwa ya shiya fitar da sabuwar waka mai taken "Ni da ku" a sabuwar shekaran nan ta 2021. 

Bayan tsawon lokaci da fitaccen mawakin ya dauka ba tare da ya yi waka ko bidiyo ba, duk da kuwa kiraye kiraye da masoyan sa su ke ta ma sa a kafafe daban daban.

Yanzu dai da alamun mawakin ya ji kiran masoyan na sa kuma hakan ya sa ya shiya sakin wata sabuwar waka a yan kwanakin nan da za su zo na farko farkon sabuwar shekarar nan da mu ke ciki. Mawakin ya wallafa wannan sanarwar ne a shafin sa na Instagram a yayin da ake tsaka da tsumayin wani sabon abu daga wajan sa a shekarar nan.

Nura M. Inuwa ya yi fice a bangaran wakokin finafinai da kuma na gama gari da su ka bashi tarin masoya da kuma arziki ta hanyoyi da dama. Nura dai kamar yadda wa su masoyan su ke masa kirari da "Sarki dan baiwa", ya kasance mawaki da ya juma ya na tashe tin bayan fitowar sa dandalin daukaka.

Kuma ya fitar da kundin album da dama a kasuwa tare da bidiyan wa su wakokin na sa da dama. Tini dubunnan masoyan sa su ke cigaba da baiyana farin cikin su da wannan labarin na sakin sabuwar waka mai taken " Ni da ku" (Me and u 2021).

Kuma za mu cigaba da bibiyan labarin dan sanin lokacin da mawakin zai saki sabuwar wakar tare da sanar mu ku da hakan. Za ku iya sauraron wakokin Nura M. Inuwa a manhajan mu ta Mdundo.com domin akwai tarin wakokin sa a kan manhajar mu.

Latest News

Ty Shaban ya fara aikin sabuwar film din sa

Umar M. Shareef ya saki sabuwar waka

 Feezy zai saki sabuwar kundin waka.

Amdaz ya na bikin zagayowar ranar haihuwar sa.

Masana'antar Hausa Hip Hop ta yi babban rashi yau.

Arewa Finext da Adam A. Zango sun saki sabuwar bidiyo

Rahama Sadau ta yi bangajiya ga mahalattan bikin dan uwan ta.

Lilin baba na shirin zagayan gidajan radiyo a Arewa.

Leave your comment