Arewa Finext da Adam A. Zango sun saki sabuwar bidiyo

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp


Matasan mawaka yan asalin jihar Kano kuma wadan da su ke karkashin kwanfanin waka ta Adam A. Zango wato "White house family", ma su suna " Arewa Finest" sun saki sabuwar bidiyo tare da babban jarumi kuma mawaki a masana'antar finafinai na Kannywood wato Adam A.

Zango mai taken "Taka" a cikin satin nan da mu ke ciki. Wakar wanda aka dauka a cikin fitaccen wajan shakatawar nan ta "Shoprite" a jihar Kano, ya samu ingantaccen aiki tare da kyakkyawan labari mai jan hankalin masoya sauraron wakokin Hausa na zamani.

Kungiyar ta mawakan su uku sun juma tare su na waka tare da fitar da bidiyoyin wadan nan wakokin. Sannan a halin yanzu su na tare ne da jarumi Zango a tin yan shekarun baya. Idan mai karatu zai tuna akwai wata waka da su ka fitar a baya chan tare da Adam Zango din da fitacen mawaki kuma mai gabatarwa a gidan talabijan ta Arewa24 wato "Nomiss Gee".

Daga dukkan alamu wannan wakar za ta samu karbuwa agun mutane sosai idan aka yi duba da shi mawakin da su ka saka a cikin wakar ta su mai taken " Taka".
Zango dai ba bako bane a wajan tallafawa kananan jarumai da mawaka a masana'antar finafinai ta Kannywood har ma da ta Hausa Hip Hop. Mawaka irin su:

Arewa Finest
Ogah Abdul
Mr Bangis
Fresh Emir
Bosskid famous
Da dai sauran su. Haka ma a bangaran finafinai akwai jarumai maza da mata sun samu tallafi ta hanyoyi daban daban wanda hakan ya sa duniya ta san su kuma su ma yanzu ake damawa da su.

Leave your comment