Umar M. Shareef ya saki sabuwar waka

By Omar Ayuba Isah

Send To A friend On Whatsapp

Fitaccen mawaki Umar M. Shareef ya wallafa sanarwar sakin wata sabuwar wakar sa da ya yi mai taken "Kar ki wuce" ta cikin film din "Sarki goma zamani goma", wacce su ka yi tare da mawakiya Khairat Kaduna".

Mawakin ya yi wannan sanarwar ne ta shafin sa na Instagram tare da kira ga masoyan sa da su nemi wannan film da ma wakar dan sauraro tare da kallon abun da ta kunsa. Shi dai jarumi Ali Nuhu ne ya bada umarni wannan film, yayin da Abubakar Bashir Maishadda ya shirya film din. Film din wanda na kwanfanin M.M Haruna ne ya samu suna mai jan hankali, wato " Sarki goma zamani goma ".

 

Inda ma su kallo da masoyan finafinan Kannywood su ke ganin zai yi kyau sosai ganin irin jarumai da kuma wadan da su ka yi aikin film din kwararru ne kuma sanannu a masana'antar. Umar M. Shareef dai ya sanu ne a Arewacin Nigeria da ma sauran kasashen duniya da ake harshen Hausa ta hanyar wakokin da ya ke a finafinai tin a farkon fitowar mawakin dan asalin jihar Kaduna. Umar ya na da masoya da dama da su ke goyan bayan sa tare da kallon sa a matsayin mawakin zamani da ba'a yi irin sa ba a tarihin wakokin rauji da aka fi sani da "Nanaye".

Yanzu haka mawakin ya kudiri aniyar sakin sabin wakoki wadan da ba na cikin film kawai ba ne irin su" Zinaru" da "Fatima Zarah" a cikin wannan shekarar ta 2021. Za mu dinga kawo mu ku wasu labaran da su ka shafi mawakin da irin wainar da ya ke tauyawa idan ana biye da mu a wannan shafin.

Leave your comment